✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jana’izar Janar Attahiru: Yadda Gwamnoni suka fusata ‘Yan Najeriya

Wasu Gwamnoni sun yi bushasha a Kano ana tsaka da jana'izar Janar Attahiru

Ran ’yan Najeriya ya baci kan yadda gwamnoni suka ki halartar jana’izar Hafsan Sojin Kasa, suka halarci daurin auren dan minista

Yayin da ake jana’izar Laftanal Janal Ibrahim Attahiru, Babban Hafsan Sojin Kasa da wasu sojoji 10 a Abuja wadanda suka mutu a hadarin jirgin sama, gwamnoni da dama sun hallara a Kano domin bikin guda cikin ‘ya’yan Abubakar Malami, Babban Attoni Janal na Kasa kuma Ministan Shari’a.

Wannan ya haifar da martani daban-daban daga ‘yan Najeriya wadanda suke ganain cewa wadannan manyan jami’an sojin da suka rasa rayukansu kan hidimtawa kasa ba a yi musu karramawar da ta kamace su ba.

Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo sun kasance ba su halarci jana’izar ba wanda ya samu halartar Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan.

Bayan hadarin jirgin a ranar Juma’a, Malami ya bada sanarwa, yana cewa ya dakatar da auren dan nasa.

Amma an yi ta murna da annashuwa a Kano lokacin da Abiru Rahman Malami, dan minista na biyu, ya yi aure a Masallacin Juma’a na Alfurqan da ke cikin garin na Kano.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci daurin auren sun hada da Bello Matawalle, na Jihar Zamfara da Aminu Tambuwal, Gwamnan Jihar Sokoto da Inuwa Yahaya, Gwamman Jihar Gombe da Abdullahi Ganduje, Gwamnan Jihar Kano sai kuma Atiku Bagudu, Gwamnan Jihar Kebbi.

Bacin rai a Soshiyar Midiya

Yadda bukin ya gudana cikin faraá da nuna annashuwa a daya gefen ba tare da nuna jimami da alhinin lamarin da ya faru ga hafsoshin sojin Najeriyar ba, ya haifar da zazzafar muhawara a kafofin sada zumunta na zamani kamar yadda za a iya ganin sakonnin Tiwita da wadansu suka wallafa.

Maybeks

@Maybeks

Yayin da kasa ke cikin jimami da alhinin Babban Hafsan Sojin Kasa da sauran manyan jami’an soja, wasu gwamonin Arewa  da abokan Attoni Janal na Tarayya, Malami sun hallara a Kano domin murnar daurin auren dansa.

Sako gami da hoton da Maybeks ya wallafa

Adamu Garba II

@adamugarba

Idan har da gaske ne a daidai lokacin da Najeriya ke cikin iftila’in da ya shafi kasar na rashin babban sadauki Janar Attahiru, amma wasu Gwamnonin Arewa suna can sun himmatu da shagulgulan daurin auren Antoni-Janar kuma Ministan Shari’ah, a kasar nan, to abin ya zama bala’i kan bala’i ke nan.

Sako mai hadi da hoto da Adamu Garba ya wallafa

 

ABDULMALIK AB

@AbdooullSG

Ke nan, Buhari bai girmama gawawwakin jaruman mayakanmu ba.


Reno Omokri

@renoomokri

A 2016, an kashe jakadan Rasha a Turkiyya, Andrey Karlov, Putin ya halarci binne shi.

A 2018, ’yan taádda sun kashe wani dan sandan Faransa, Arnaud Beltrame, Macron ya halarci binne shi.

A Najeriya, mun yi rashin Babban Hafsan Sojan Kasa, inda @OfficialAPCNg Gwamnoninmu suka yi dabadala Kano!

Hoton da Reno Omokri ya wallafa
Sako mai hade da hoton da Reno Omokri ya wallafa

Wajen binne mamatan

Koda yake za a iya cewa ba a taru aka zama daya ba, wasu manyan jami’an gwamnatin sun girmama jami’an sojin da suka kwanta dama inda suka halarci  wajen.

Cikinsu akwai Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno da Nasir El-Rufai  na Jihar Kaduna da Mai Mala Buni na Jihar Yobe.

Ministan Sadarwa, Lai Mohammed da Ministan Tsaro, Bashir Magashi da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari sun halarci jana’izar.

Yayin da Babban Hafsan Hafsoshi, Janal Lucky Irabor da Hafsan Sojin Ruwa Rear Admiral Awwal Gambo, da Mukaddashin Sufeta Janal na ’Yan Sanda, Usman Baba, suma suka halarci jana’izar a Abuja.