✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jan-baki: An fara yi wa tsuntsayen da suka addabi gonakin Kebbi feshi ta sama

Tsuntsayen dai kan cinye amfanin gona gaba daya

Gwamnatin Jihar Kebbi ta fara feshi ta sama kan tsuntsayen jan-baki da suka addabi gonakin manoma a Jihar.

Ana feshin ne kan tsuntsayen da ke yin hijira a Kananan Hukumomin da suka fi kamari na Argungu da Bagudu da kuma Kalgo.

Gwamnan Jihar, Dokta Nasir Idris, yayin kaddamar da fara feshin ya ce sun fara shi ne domin tabbatar da samar da abinci a Jihar.

Nasiru Idris dai ya sami wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Yakubu Bala Tafida, a lokacin kaddamarwar.

Gwamnan ya ce, “Wadannan tsuntsayen, musamman na jan-baki na da matukar barazana wajen samar da abinci, musamman hatsi.”

Ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sa kafar wando daya da duk wata matsala da za ta zama barazana ga nasarar da fannin aikin gona yake samu a Jihar.