✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jamus ta kwace jirgin ruwan wani attajiri dan kasar Rasha

Darajar jirgin ruwan ta kai kusan Dala miliyan 600.

Hukumomin Jamus sun karbe wani katafaren jirgin ruwa na alfarma da darajarsa ta kai kusan dala miliyan 600 mallakin wani hamshakin attajiri dan kasar Rasha, Alisher Usmanov.

Rahotanni sun bayyana cewa mahukuntan na Jamus sun kwace jirgin ne a wata tashar jiragen ruwa da ke Hamburg.

Usmanov na cikin jerin attajiran da za su fuskanci takunkumi daga Tarayyar Turai a matsayin martani na mamayar da dakarun sojin Rasha suka yi wa Ukraine tun a ranar 24 ga watan Fabrairu.

Jirgin ruwan da ake kira da Dilbar mallakar Alisher Usmanov

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Ministan Kudin Faransa, Bruno Le Maire, ya ce ya kame wani katafaren jirgin ruwa da ake alakanta shi da wani hamshakin attajiri dan kasar Rasha, Igor Sechin a tashar ruwa ta La Ciotat da ke gabar tekun Bahar Rum.

Jirgin ruwan Igor Sechin da Faransa ta kwace

Ma’aikatar Kudin Faransar ta ce jirgin ruwan mallakar wata kungiya ce wacce aka bayyana Sechin a matsayin babban mai hannun jari a cikinta.

Wani rahoto da Mujallar Forbes ta fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa mahukuntan Jamus sun kame jirgin ruwan da ake kira Dilbar mallakin Alisher Usmanov mai tsawo mita 156-kimanin kafa 512, darajarsa ta kai Dalar Amurka miliyan 600 wanda ake daukarsa a matsayin jirgin mafi girma a duniya ta fuskar tsada.