Jam’iyyun PDP, da LP da kuma ADC sun bukaci da a sake gudanar da sabon zaben Shugaban Kasa da aka gudanar a ranar Asabar, suna masu cewa zaben na cike da kura-kurai.
Shugaban jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu da sauran takwarorinsa na ADC Ralph Nwosu da Julius Abure na LP, sun bayyana haka ne a wani taron manema labarai da suka kira a Abuja yau Talata.
- Gwamnoni 7 da suka gaza kai bantensu Majalisar Dattawa
- PDP ta kwace duk kujerun sanatocin APC a Kaduna
Jam’iyyun sun yi zargin cewa jami’an INEC sun tafka magudi a zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisar Tarayya da aka gudanar ta hanyar kin saka sakamakon zaben a shafin hukumar.
“Babu gaskiya a cikin wannan zabe, ana kuma ci gaba da soke sakamakon zabe a yankunan da jam’iyyun adawa ke da karfi,” in ji Abure.
Sun kada kuri’ar yankan kauna kan Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, inda suka yi kira da ya gaggauta sauka domin wani ya maye gurbinsa da kuma gudanar da sabon zabe.
Jam’iyyun sun ce ba za su aminta da aiwatar da bukatar saka sakamakon zabe a shafin hukumar zabe ba da shugabanta ya yi wanda kuma yake cikin sashi 60 na Dokar Zabe ta 2022.