Wani matashi mai shekara, Musa Lawan, ya kayar da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Hon. Ahmad Lawan Mirwa, da ke neman tazarce a majalisar.
Rahotonni na nuna cewa matashin da ya lashe zaben dan PDP ne, kuma wannan ne karo na biyu da suka fafata da Ahmad Lawan, wanda ya shafe shekaru 20 a majalisar.
- Jami’an tsaro sun datse hanyar zuwa Hedikwatar INEC a Kano
- Majalisa ta 10: Ba mu tsara yadda za mu raba mukamai ba —Abdullahi Adamu
Jami’in tattara sakamakon zaben Mazabar Nguru, Dokta Habib Muhammad ya bayyana cewa matashin ya ci zaben ne da kuri’u, 6,648, yayin da shugaban majalisar ya samu Kuri’u 6,466.
Wata majiya da ke garin na Nguru ta bayyana wa Aminiya cewa, an kusa samun ’yar hatsaniya a mazabar, sakamakon jinkirin sanar da wanda ya lashe zaben, har sai da matasa suka yi barazanar cinna wuta a ofishin tattara sakamakon zaben.
Ganin hakan ya sanya jami’an Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) suka sanar da sakamakon da ya nuna matashin ne ya yi nasara.