✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyu 10 sun shirya taron dangi a zaben Ondo

Wasu jam’iyyun siyasa goma sun amince su yi taron dangi ta hanyar tsayar da dan takara daya a zaben Gwamnan Jihar Ondo da ke tafe.…

Wasu jam’iyyun siyasa goma sun amince su yi taron dangi ta hanyar tsayar da dan takara daya a zaben Gwamnan Jihar Ondo da ke tafe.

Jam’iyyun sun yi hakan ne karkashin inuwar ja’iyyun da hukumar zaben ta kasa (INEC) ta yi wa rajista (CIRPP) gabanin zaben na ranar 10 ga Oktoba, 2020.

“Nan da sa’a 72 masu zuwa CIRPP za ta sanar da matsayinta game da wanda za ta mara wa baya”, inji hadakar.

Manayan ‘yan takara a zaben sun hada da gwamna Rotimi Akeredole na jam’iyyar APC, da Eyitayo Jegede da PDP da kuma Agboola Ajayi na ZLP.

Da Suke sanar da hakan bayan taronsu a Legas a ranar Alhamis, Shugaban Jam’iyyar SDP, Olugbemi Ogubameru da Sakataren Jam’iyyar AAC da sauran masu hadakar sun ce ba su kai ga zabar wanda zai yi musu takara ba tukuna.

Sanarwar tasu na dauke da sa hannun Ajibola Falaiye (Accord), Olaoluwa Adesanya (APP), Cif Tokunbo Adetoro (ADC) da Prince Niran Toyin (APGA).

Sauran su ne Mista Felix Funso Oloro (APM), Olagookun Peter (NNPP), Misis Funmilayo Ataunoko (NRM) da kuma Mista Amos Agunloye (LP).