✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyar PDP ta yi hantsal-batsal

Tabbas ‘yan magana sun yi gaskiya da suke cewa,”duk abinda ka gani ya baka tsoro! Wata rana zai ba ka tausayi”. Don haka dangane da…

Tabbas ‘yan magana sun yi gaskiya da suke cewa,”duk abinda ka gani ya baka tsoro! Wata rana zai ba ka tausayi”. Don haka dangane da rikicin PDP, da darewarta gida biyu wallahi bai zo mana da mamaki ba, domin mun sani komai daren dadewa tilas sai haka ta faru, amma sai dai ba mu yi tsammani abin a kusa yake ba. Saboda ikirari da har kullum suke yi, kuma ba su daina ba, na cewa “wai shekaru 60 za su yi suna mulki”. Sannan kuma ni  tambayar da nake so su ‘yan PDP su amsa mini ita ce:”Wai da wannan hantsal-batsal din rikicin ne za su sami damar iya murdiyar zabe da suka saba?”  Daga Basheer Mukhtar Yusuf Zaria. 07034514844

Sakonnin waya

Ga Isa Yuguda
Sallam Malam Isah Yuguda Allah ya saka maka da aljanna. Yanzu cikin Bauchi ba ambaliya tun da ka jagoranci talakawan ka aka tsafce magudanan ruwa. Daga Armaya’u 080396674777.

APC jama’iyyar Sakkwatawa
Sunjiya ga jikinsu don ’yar manuniya ta nuna alamar haka sai a tabon Garkuwan Sakkwato. Ni Mustapha shaida ne na gani a idona, kuma talakawa sun shaidi haka. Fatarmu kawar da mutanen  banza a Jihar Sakkwato. Daga Musty Sok 08034068363.

Ga Ali Nuhu
Zuwa ga Ali Nuhu shawarata a gareka ita ce kada neman kudinka ya janyo maka sabawa da Mahaliccinka. Ba tun yau nike ganin kana hada kanka da wani jinsi wanda ba naka ba. A bangaren sana’arka, ka yi hankali. Daga AbdulAzeez Maska Funtua 07068549745.

Shawara ga Attahiru Jega
Idan Allah Ya kaimu 2015 ya kamata a hada zaben shugaban kasa da na gwamnoni lokaci guda, domin hana a ringizon kuri’a. Daga Abdullahi Babangida 080387784550

Ga ’yan damfara
Edita ina kira ga ’yan damfara da ’yan mata mayaudara da su daina daukar lambobin mutane a wannan shafi suna cutar da su, domin haka ya faru da ni; daga damfarar har yaudarar. Sai a yi hattara. Daga abdulAzeez Maska Funtua 07068549745.

Ga Tata Katsinawa
Mutanen Jihar KAtsina, Allah Ya bar Umar Abdullahi Tsauri, wato Tata. Umaru ya tafi, Umaru ya dawo. Daga Matasan Tata Na Bakori. Baban Khadija Mai Allah, Alhaji Mudansir Mukhtar Madawakin Bakori 07063102009.

Hattara matasa
Matasa mu yi wa Allah da ManzonSa, mu kama aikin yi, mu rabu da harkar jagaliya, ko sara suka. Daga Com. Yakubu Skido Lagos Mile 12. 08060777062.
Godiya ga Sakkwatawa
Salam. Don Allah Edita ka isar min da goron godiyata a daukacin miliyoyin al’ummar Jihar Sakkwato a bisa ga gagarumin tarbar da suka yi wa Janar Muhammadu Buhari (Mai-Gaskiya) a ranar Asabar din da ta gabata. Allah Ya ja zamanin Mai-gaskiya, tare da nasara. Amin. Daga Aliyu B. Aliyu Bakura. 08051755591.

Muna nan a PDP
Edita, muna nan a jam’iyyarmu ta PDP har sai azzaluman cikinta sun gane gaskiya. Duk wani dan Najeriya ya san cewa jam’iyyar PDP an kafa ta ne a kan gaskiya. Muna nan a cikinta, muna bayanka Dokta Sule Lamido kar ka ba shi kofa. Daga Ahmad Dawakin Kalgwai 08032323437.

Alhaki ya kama PDP
Lallai jam’iyar PDP alhakin jama’a ya kama ki, har kin kai ga rabuwa biyu, to sauran uku har 4, har 100. Kai sai kin rabu kaca-kaca ba biyu ba. Daga AbdulAzez Maska Funtuwa 07068549745.

Ga Aminiya
 Assalamu alaikum. Aminiya ina kira ga mahukuntan Najeriya da su gagauta janye jami’an tsaro daga yankin Arewa maso gabashin Najeriya, musamman jihohin Barno da Yobe. Wallahi cin zarafin da suke aikatawa a kan fararen hula ya yi yawa. Daga dahiru dauda (KGY) Bindawa 08092115592.

Ga Bafarawa
Salam Aminiya. Idan ka shuka alheri, to ko baka nan sai an ambace ka da alheri. Kuma ka samu addu’a daga masoyanka. Bafarawa abin da ka yi muna Sakkwato ba za mu manta ba. Allah Ya kareka daga shairin makiya da mahassada, Allah Ya daukaka darajarka a duniya da lahira. Amin. Daga Kabiru M. Sakkwato 08154872959.

Ga Gwamonin Arewa
Lokacin sallah gwamnonin Arewa kuka ki biyan ma’aikata albashi. Allah wadaran naka ya lalace. Daga Ali NCC Money 08033096609
Addu’a ta kama PDP
Addu’ar talakawa ta kama jam’iyyar PDP. Allah ya ba mu shugabanni nagari wadan da za su ci gaba da ceto kasar nan akan halin da ta shiga yanzu. Daga kasimu Aliyu Sardaunan Matasan Assada, Sokoto. 08034376194.

Hattara da PDP
’ Yan’Najeriya masu murna wai jam’iyar PDP ta dare gida 2.To yakamata ku bar murna da hakan, domin PDP-PDP ce. Wani sabon salo ne na yau darar ku da za ta yi a zaben 2015. Ya kamata wanda maciji ya sara in ya ga tsumma ya ruga! Da fatan za ku yi hattara. Daga Haruna Muhammad Katsina.07039205659.

Jinjina ga Sarkin Katsina
Allah Ya kara wa Mai martaba  Sarkin Katsina Dokta AbdulMumin Kabir Usman lafiya. Amin. Daga Nura Garba Shigifa Mani 07039336645.
Daga Shehu danfodiyo
Shehu danfodiyo ya ce: “Shugaba kan samu nasara a kan abokan gabarsa ne ta hanyar kyautata adalcin da yake yi wa al’ummarsa, kuma ana yin nasara a kansa ne ta hanyar rashin adalcinsa.” Don haka shugabanni a rungumi adalci a yada zalunci. Allah Ya sa su gane hakan! Daga Usman 08070921745.

Muna neman canji
Allah Ka kawo mana canji a Najeriya. Daga Babangida A Gilo Ilorin Jihar Kwara 08161677650.

Cutar wariya a PDP
Aminiya, mun fara ganin cutar wariya da ta kama PDP. Allah Ya yi wa ’yan Najeriya maganin PDP, Ya kuma zaba mana shugabanni nagari. Amin. Daga Aliyu Abba PRP 08136731410.