A ranar Asabar 9-12-2017, babbar jam’iyyar adawa ta PDP da ta mulki kasar nan har tsawon shekaru 16, tun bayan da aka dawo mulkin dimokuradiyya a kasar nan a shekarar 1999 zuwa 2015, ba kakkautawa, ta gudanar da babban taronta don zaben shugabannin da za su ja ragamarta nan da shekaru hudu masu zuwa in Allah Ya kaimu. Yin wancan babban taro ya biyo bayan fita da jam’iyyar ta yi na rigingimun shugabanci tun bayan faduwar zaben da ta yi a shekarar 2015 din. Rigingimun da tushen su faduwarta wancan babban zabe, wanda bayan faduwarshi ne shugabanta da ya jagorance ta zuwa babban zaben Alhaji Ahmed Adamu Mu’azu, wanda tsohon Gwamnan Jihar Bauchi ne tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, da rana tsaka ya ce ya sauka daga kan shugabancin jam’iyyar bisa ga lalurar rashin koshin lafiya da likitocinsa suka ce da shi yana bukatar hutawa.
Saukarsa ke da wuya bayan wani lokaci na rikon mukkadashin shugaban jam’iyya Yarima Uche Secondus a zaman shugaba na wucan gadi, aka nada Alhaji Ahmed Muhammad Makarfi a zaman shugaban kwamitin rikon kwarya an kuma dora masa alhakin gudanar da babban zaben jam’iyya don zaben sababbin shugabanni. Daga bisani a taron da jam’iyyar ta shirya a garin Fatakwal babban birnin Jihar Ribas a wani lokaci cikin shekarar 2016, can aka yi zube ban kwaryata, inda Sanata Ali Modu Sharif ya karbe shugabancin jam’iyya, rigimar da kotun kolin kasar nan ta kawo karshenta a ‘yan watannin baya, bayan da ta tabbatar da cewa shugabancin riko na Sanata Makarfi shi ke halartattacen kwamitin rikon jam’iyyar, ba na Sanata Ali Modu ba.
Samun wancan hukuncin ya sanya jam’iyyar ta PDP ta hanzarta ta gudanar da wancan babban taro, inda ta zabi sababbin ‘yan kwamitin zartarwa na kasa a ranar 9 ga wannan watan na Disamba. A wancan babban taro ne jam’iyyar ta zabi Yarima Uche Secondus daga shiyyar Kudu maso Kudu, wanda dama shi ne mukaddashin shugaban jam’iyya na kasa baki daya, daga cikin ‘yan takara 9, da tun farko suka nuna kwadayinsu na zama shugaban jam’iyya, wanda 7, daga cikinsu sun fito ne daga shiyyar Kudu maso Yamma, shiyyar da aka shirya cewa a zaben Fatakwal da ya yiwu da ita za a ba shugabancin jam’iyya na kasa baki daya.
Amma abin ka da harkar shiyasa wancan rigima da jam’iyyar ta fada ta sanya aka canja lale, ta yadda gwamnonin jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike suka canja wancan tsari na ba da shugabancin a shiyyar Kudu maso Yamma, suka karkata shi zuwa shiyyar Kudu maso Kudu. Dama can a karkashin raba mukaman jam’iyyar da aka yi an ba jihohin Arewa damar su za su fitar da dan takarar neman shugabancin kasa a inuwar jam’iyyar ta PDP a kakar zabe ta 2019 in Allah Ya kaimu.
Akwai maganganu guda uku da ake zargin su suka haddasa wancan canji na ba Kudu maso Kudu shugabancin. Na daya ana zargin canjin shekarar da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya yi daga jam’iyya mai mulki ta APC (da ya zauna cikinta har shekaru hudu bayan ya bar jam’iyyarsa ta asali wato PDP), ta sanya gwamnonin PDP zargin jiga-jigan jam’iyya na bayan fage irinsu tsohon shugaban kasa na mulkin soja Janar Ibrahim Babangida su na da aniyar ganin ta kowane hali Atikun za su tsaida takarar neman shugabancin kasar nan a zaben mai zuwa. Batu na biyu shi ne su kuma gwamnonin PDP su na ganin zuwa yanzu sun kawo karfi, da ganin su ke da jama’a don haka ba za su bi tsohuwar tafiya ba. A bisa ga wannan tunani na su na kasuwar bukatarsu ta shigo a kan daga Arewa duk da akwai ‘yan jam’iyyar irinsu tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma tsohon Ministan ilmi Malam Ibrahim Shekarau da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido da tuni a rubuce suka aika wa uwar jam’iyyar aniyarsu za su nemi takarar shugabancin kasa, amma sun fi goya wa tsohon shugaban kwamitin rikon jam’iyya Sanata Makarfi da ake zargin shi ma yana kwadayin jam’iyyar ta tsayar da shi takarar neman shugabancin kasa, ta yadda in haka ta samu zai dauko Gwamnan Jihar Ribas din ko na Jihar Ikiti Ayodele Fayose ya rufa ma sa baya.
Masu iya magana kan ce “Ba a san ma ci tuwo ba sai miya ta kare,” yadda aka gudanar da zaben ta hanyar fitar da wani jadawalin wadanda suka yi takara, kuma dukkan su suka samu nasara da sunan jerin sunayen hadin kai, ya bakanta wa jiga-jigan jam’iyyar PDP na shiyyar Kudu maso Yamma da a da aka kwadaitama ba su mukamin shugabancin jam’iyyar, amma duk da wasu ‘yan takarar su sun janye su bar wa Furofesa Tunde Adeniran tsohon Ministan ilmi, amma dai bai kai labari ba. An ce gwamnonin da suka kitsa hakan cikin su kuwa har da Gwamna Fayose da ya fito daga jiha daya da Furofesa Adeniran, bayan sun yi haka ne a kan kasuwar bukatar kansu, sun kuma yi la’akari da cewa shiyyar ta Arewa maso Yamma (kasar Yarabawa), ita kadai ce shiyya cikin shiyyoyin kasar nan shidda da take siyasa a kan akidar me jagora ya ce, kamar yadda tarihi siyasar kasar nan yake tabbatarwa tun daga jamhuriya ta daya zuwa yanzu. Sabanin sauran shiyyoyi kasar nan da suke tamfar ballagaza a harkar siyasar.
Yanzu abin da ake hasashe a tafiyar jam’iyyar PDP din zuwa babban zaben shekarar 2019, da aka tabbatar da cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar koda ana ha maza ha mata, zai nemi takarar mukamin shugabancin kasar nan, a gefe daya kuma ga mutane irinsu Malam Ibrahim Shekarau da Alhaji Sule Lamido da tuni suka bayyana bukatarasu, da ma wadanda kila suka iya fadowa cikin fagen nan gaba, nasarar jam’iyyar za ta dogara ne kacokan akan wane ne ta tsayara dan takara daga Arewa, kuma daga wacce shiyya ta dauko mai rufa masa baya, shiyyar Kudu maso Gabas (ta ’yan kabilar Igbo) da jihohinsu hudu duk PDP suke yi ko ta shiyyar Kudu maso Kudu da PDP tafi karfi.
Ko su wa PDP din ta yanke shawarar tsayarwa a takarar neman shugabancin kasa da mai rufa masa baya, lallai kullum ta rinka tunanin har yanzu talakwa masu bin layi su kada kuri’a, musamman na Arewacin kasar nan suna nan tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC kuma su na yi masa addu’ar Allah Ya kara ba shi lafiya Ya kuma karfafeshi da ya sake tsaya zaben 2019, shi za su zaba, kasancewar sun fara gane irin mawuyacin halin tabarbarewar tattalin arzikin kasa da na matakan tsaro, musamman rikicin Boko Haram da aikin yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatinsa take ta fama da su da kuma irin nasarorin da yake samu akansu.