Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kano ta ce ta shirya tsaf domin magance abin da ta kira cin zarafi da wulakacin da jam’iyya mai mulki ta APC ke shirin yi wa ’ya’yanta.
Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Alhaji Shehu Wada Sagagi ya fitar.
- Idan za a yi gaskiya a zaben kananan hukumomin Kano PDP za ta sami nasara – Doguwa
- PDP ta kaurace wa zaben kananan hukumomin Kano
- Zaben Kananan Hukumomi: Rikici ya barke a jam’iyyar APC reshen Kano
- Zaben Kano: babu wani dalilin soke zabe – APC
Sagagi ya yi mai da martani ne game da wasu kalamai da Shugaban Jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas ya yi a wani sakon bidiyo.
Abdullahi Abbas, ya ce yanzu suka fara magudin zabe, kuma za su ci gaba da yi ba za su bari ’yan Kwankwasiyya su sake samun tasiri ba.
Abbas a cikin bidiyon ya yi barazana ga ’yan PDP, inda ya ce duk inda magoya bayansu suka gan su su sa musu duka.
Sai dai shugabancin PDP a jihar, ya ja hankalin jama’a cewar zaben 2019 da aka yi, an shirya magudi ne inda aka sanar da zaben a matsayin wanda bai kammala ba.
Ya ce sun shirya tunkarar duk wata barazana da za su fuskanta a kakar zabe mai zuwa daga jam’iyyar APC.
Daga karshe Sagagi ya yi kira ga Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, da Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, da sauran hukumomin tsaro da su zama shaida a kan kalaman Abdullahi Abbas.