Tsohon Gwamnan Sakkwato kuma jagoran jam’iyyar APC a Jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya ce za su kara karfi bayan kammala rajistar mambobin jam’iyyarsu da ake kan gudanarwa.
Wamakko ya furta hakan ne a lokacin da ya sabunta rajistarsa a rumfar zabe ta Gidan Ja’oje mai lamba 003 a Karamar Hukumar Wamakko da ke Jihar Sakkwato.
- Ali Jita: Kannywood ta girgiza da rasuwar mahaifinsa
- Maciji ya kashe mutum 7, 15 sun kamu da ciwon kafa
- Yadda Rikadawa ya martaba yaronsa da auren ’yar cikinsa
Sanata Magatakarda ya ce dangane da batun rashin sauya shugabanni a jihar, an yi haka ne domin ciyar da jam’iyyar gaba da nufin inganta shirinta na tunkarar zaben 2023.
Ya ce da ikon Allah jam’iyyar za ta samu nasara a zaben mai zuwa a matakin jiha da kasa.
Ya jinjina wa shugabannin jam’iyyar da suke tafiyar da ita a bisa turbar da ta dace tun bayan nada su har ya zuwa yanzu.
Da yake amsa tambayar shin ko jam’iyyarsu za ta shiga zaben Kananan Hukumomin da za a gudanar ya ce “saboda mi ba za ta shiga ba?”
A nasa jawabin, shugaban raba katin da uwar jam’iyyar ta turo Sakkwato, Farfesa Saleh Muhammad ya ce APC dangi daya ce kuma uba daya.