Jam’iyyar APC ta nuna takaicinta bisa yadda aka kutsa cikin Majalisar Dattawa aka sace sandar majalisar.
Mai magana da yawun jam’iyar, Malam Bolaji Abdullahi ne ya sanar da hakan a lokacin da yake jawabi a madadin jam’iyyar a game da matsayarta a kan sace sandar da aka yi da safiyar yau din nan, inda ya ce sace sandar ba kamarin cin fuska bane da majalisar.
Sannan kuma jam’iyyar ta bukaci jami’an tsaro da suk dauki duk matakan da ya kamata su dauka domin kama wadanda suke da hannu a wannan lamarin.