✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam`iyyar APC na dambarwa ne tsakanin Gwamna Kwankwaso da Malam Shekarau a Jihar Kano?

A ranar Alhamis din makon jiya ne, uwar jam`iyyar APC ta tura wani kakkarfan ayari, a karkashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Edo, Cif John Oyegun…

A ranar Alhamis din makon jiya ne, uwar jam`iyyar APC ta tura wani kakkarfan ayari, a karkashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Edo, Cif John Oyegun zuwa Kano don ba tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau hakuri kan abin da shugabannin jam`iyyar suka gano na kuskure a wata ziyarar zawarcin da suka kai wa Gwamna Rabi`u Musa Kwankwaso.
  Idan mai karatu bai manta ba, a kwanakin baya ayarin uwar jam`iyyar ta APC da ya kunshi iyaye da shugabanni da wasu daga cikin gwamnonin jihohi na jam`iyyar, sun rika kai ziyarar zawarci ga gwamnonin jam`iyyar PDP bakwai da ake ma lakabi da ‘G7’. Wasu daga cikin irin mutanen da ayarin APC din yakan kunsa zuwa jihohin, sun hada da Janar Muhammadu Buhari da Alhaji Ahmed Bola Tinibu da Cif Bisi Akande da Alhaji Aminu Bello Masari da wasu daga cikin gwamnonin jam`iyyar APC din.
A bisa ga tsarin da aka kafa jam`iyyar APC, an damka jagorancinta a kowace jiha ga gwamnan jiha, a inda take da gwamna, ko kuma ga tsohon gwamna, a inda ba ta da mulki, don haka a waccan ziyara ta Kano da shugabannin APC suka kai, rashin ganin jagoran jam`iyyar na jihar wato Malam Ibrahim Shekarau tare da ayarin ya sanya manya da kananan  magoya bayan APC a jihar, musamman magoya bayan shi Shekarau, tunanin tamkar an mika jagorancin tafiyar APC din ga Gwamna Kwamkwaso, duk kuwa da sanin cewa Malam Shekarau ne jagora.
Abinka da harkar siyasa, sai ake ta ba shi ma`anoni iri-iri a kafofin yada labarai da ke jihar, har wasu na cewa APC din ba ta yi da tsohon gwamna Shekarau, don haka ta rungumi Gwamna Kwankwaso, alhali a jin kunnen `yan PDP Kwankwasiyyar da mutanen jihar da ma na kasa baki daya sun ji Gwamna Kwankwaso yana fada wa ayarin na APC cewa batun ya amsa gayyatarsu ta ya dawo APC, ba nasa ba ne shi kadai, don haka yana bukatar lokaci da zai tuntudi dukkan masu ruwa da tsaki a cikin tafiyar ta sabuwar  PDP, kafin yanke hukunci.
Wannan rudani da aka samu, ya sanya uwar jam`iyyar ta APC, ta turo  wancan ayari na Cif John Oyegun,wanda ya kunshi Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdulazez Yari da Alhaji Aminu Bello Masari da Alhaji Yusufu Ali, tsohon shugaban rusasshiyar jam`iyyar APP. Da yake jawabi a gidan Malam Shekarau da ke kan titin Mundubawa, a cikin unguwar Nassarawa ta kewayen birnin Kano, Cif Oyegun ya fadi cewa shi da Cif Tinubu da Alhaji Aminu Masari sun kai ziyara ga Malam Shekarau a masaukinsa na Abuja, inda suka nuna masa damuwarsa kan irin bacin ran da ziyarar tasu ta Kano ta haddasa tsakanin `yan jam`iyyarsu.
Cif Oyegun ya ce tun a Abujar Malam Shekarau ya fahimci hamzarinsu, amma kuma ya nemi jam`iyyar da lallai ta tura wani ayari Kano don ya ba mutane da `yan jam`iyyar da magoya baya hakuri kan abin da aka yi, al`amarin da ya kai su Kano. Ya tabbatar wa Malam Shekarau da `yan jam`iyyar APC da magoya baya da ma sauran al`ummar jihar cewa Malam Shekarau shi ne shugaba kuma jagoran tafiyar jam`iyyar APC a jihar. Haka su ma dukkan wadanda suka yi  jawabi a gidan, kwatankwacin irin wannan jawabin ba da hakuri da tabbacin goyon baya ga Malam din suka yi.
Da yake mayar da martani, Malam Shekarau ya fada wa ayarin cewa ba shi da haufi kan wanda duk ke son ya shigoAPC, amma dai abin da ke tabbatacce a jihar, shi ne ba wanda zai iya ja da rusassun jam`iyyun nan uku a jihar ta Kano, wato ANPP da ACN da CPC da suka taru suka kafa jam`iyyar APC, ya kara da cewa ko da wai bai damu da ziyarar da aka kai wa Gwamna Kwankwaso ba, amma abin tambaya, shi ne akwai bukatar a kai ziyarar?
Tun  a wajen shekarar 2002, lokacin da Gwamna Kwankwaso yake mulkin Jihar Kano a karon farko, aka fara takin-saka tsakaninsa da Malam Shekarau, lokacin da Malam yake babban sakatare a gwamnatin, ya kuma fara nuna kwadayinsa na neman gwamnan jihar a zaben 2003, al`amarin da Kwankwaso ya kasa hakuri a kai.  karshe ya cire Malam daga mikaminsa ya mayar da shi Kwalejin share fagen shiga jami`a ta jihar a zaman malamin lissafi.
Daga wannan matsayi Malam Shekarau ya ajiye, ba don yana so ba, ko kuma lokacin hakan ya yi ba, illa dai matsin lambar gwamanatin Kwankwaso ya ishe shi, ta yadda ko da ya ajiye aikin, ya shiga fagen takarar neman mukamin gwamnan jihar a inuwar jam`iyyar ANPP, an ce gwamnatin Kwankwason kin biyansa kudadensa na ajiye aiki ta yi, bare kuma fenson wata-wata.
Allah cikin ikonSa, ya nuna Shi ke ba da mulki ga wanda Ya so a lokacin da Ya so, Ya sa Malam Shekarau ya kayar da Gwamna Kwankwaso a zaben shekarar 2003. Zuwan Malam Shekarau ke da wuya a kan karagar mulki, sai ya kafa kwamitin bincike a kan gwamnatin Kwankwaso, kwamitin da ya yi nasarar kwato makudan kudade ga wasu jami`an gwamnatin ta Kwankwaso.
   Mai karatu za ka iya gane cewa a yadda ake siyasar zaman doya da manja a Kano tsakanin Gwamna Kwankwaso da tsohon gwamna Shekarau, kowa sarki ne a cikn siyasar jihar Kano. Bisa ga wannan adawa mai tushe dake tsakanin jiga-jigan biyu da irin yadda ita kuma jam`iyyar APC, ta yunkuro a wannan karon da aniyar lalla a zabubbukan 2015, ta karbe mulki a dukkan jihohin PDP da ma kasa baki daya, don haka duk wanda take ganin zai iya kai ta ga nasara shi za ta bi, amma dai a kan jihar Kano da zabubbukan 2015, lallai akwai bukatar jam`iyyar APC ta yi mutunci wanda `yan siyasar kasar nan ba su gada ba, ta zauna gidan da take ta saurari sarautar Allah a kan zabubbukan 2015, a kan Jihar Kano kar ta bata rawarta da tsalle. Mulki na Allah ne!