✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’o’in Arewa 3 za su ci gajiyar shirin Bankin Duniya

Jami'ar ABU, ATBU da FUAM za su ci gajiyar shirin SPESSE na Bankin Duniya.

Jami’o’in Arewa uku sun shiga jerin jami’o’i shida da suka yi zarra a fannin bincike da ilimi mai zurfi da za su amfana da shirin Bankin Duniya.

Hakan na zuwa ne a yayin da Gwamnatin Tarayya da Bankin Duniya suke shirye-shiryen fara aiwatar da shirin kare muhalli da inganta yanayin rayuwa (SPESSE) da zimmar samar da kwararru daga cikin gida a fannin, inda aka zabo jami’o’in Arewa da Kudu guda shida da suka yi zarra a Najeriya.

Jami’o’in da suka ciri tutu a yankin Arewa su ne: Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ta Bauchi (ATBU), Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU) da Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Makurdi (FUAM).

Daga yankin Kudu kuma akwai Jami’ar Kere-kere ta Tarayya da ke Owerri (FUTO); Jami’ar Benin (UNIBEN) da kuma Jami’ar Legas (UNILAG).

An tsara shirin SPESSE, wanda ke da tallafi daga Bankin Duniya ne domin bayar da horo da samar da kwarewa ga daliban jami’a a matakai daban-daban a fannin bincike da kare muhalli da kyautata rayuwa.

Manufar shirin ita ce bunkasa yanayin rayuwar jama’a, kare muhalli, da kuma samar da adalci da shugabanci na gari a bangaren gwamnati da kamfanoni

Shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC), Farfesa Abubakar Rasheed, ya ce an zabi jami’o’in su zama cibiyoyin aiwatar da shirin ne bayan zuzzurfan bincike da kwararru daga bangarori daban-daban suka gudanar bisa dogaro da manhajar karatu ta NUC.

Shugaban SPESSE na Bankin Duniya, Cif Bayo Awosemusi, ya ce shirin shi ne irinsa na farko a duniya da ma Najeriya a matsayin giwar Afirka, wadda jami’o’in kasar shida suka zama cibiyoyin aiwatar da shirin.

A ranar Alhamis Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, zai jagoranci bude shirin a Abuja, inda za a kulla kawance da masu bayar da tallafin kudaden bincike da masu binciken daga jami’o’in da suka yi zarra.