Jami’o’i a Najeriya za su fara yajin aiki da zarar an bude su saboda matsalar da ta ki ci, ta ki cinyewa tsakaninsu da gwamnati.
Ma’aikatan jami’o’in sun ce sun gaji da jan kafar gwamnati wajen biyan bukatunsu na gyaran albashin da makarantun bayan yarjejeniyar da suka yi.
“Muddin aka bude jami’oi daga kullen COVID-19 ba tare da an yi abin da ya dace ba, to babu makawa yajin aiki za mu fara.
“Abin da muke so a kawar ke nan shi ya sa muke kiran gwamnati ta yi abin da ya dace tun da wuri”, inji Samson Ugwoke, Shugaban hadakar aiki da cikawa na kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i (JAC).
Game da hakkokinsu na karin albashi, sun ce, “Jan kafa na fiye da shekara daya bayan an aiwatar a wasu bangarori shaida ce cewa jami’o’i sun yi hakuri sosai”.
Kungiyoyin Ma’ikatan Jami’o’i (NASUU) da ta Malaman Jami’o’i (SSAU) a taronsu na ranar Alhamis sun ce, “Hakan bai dace ba”.
Bukatunsu su ne gwamnati ta fitar da su daga tsarin albashi na (IPPIS), ta kuma cika musu kudandan da suke bi na karin albashi.
Sauran sun ne rashin wadatar da jami’oi mallakar jihohi da kudade da kuma rashin kwamitocin ziyartar su domin sanin bukatunsu.
Suna kuma zargin gwamnati ta rashin mayar a hankalin wajen sabunta yarjejeniyar bangarorin na shekarar 2009 kan bukatun jami’o’i.
Sanarwar da suka fitar na dauke da sa hannun Shugaban SSANU na kasa Samson Ugwoke, da babban Sakatren NASU, Peters Adeyemi.
Ugwoke ya ce duk da wasikun da suka yi ta aika wa ofishin IPPIS tun watan Fabrairu, har yanzu matsalolin da ‘yan kungiyar ke fuskanta na nan.
Don haka suke so a tsayar da shi domin a cewarsu ba shi da amfani saboda yadda ‘yan kungiyar ke samun matsala da albashinsu.
“Muna ka ‘yan Najeriya masu fada a ji da su ja hankalin gwamnati ta gyara kurakuran da ke cikin IPPIS.
“A biya mu bashin da muke bi na alawus din mu da karin albashi da sauransu”, inji shi.