Jamilu Isiyaku da ke neman takarar kujerar Gwamnan Jihar Gombe a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya nemi ’yan jam’iyyar da su yafe masa ficewa da ya yi daga cikinta a 2019 saboda rashin samun tikitin takara.
Dan siyasar wanda ake yi wa lakabi da Jamilu Gwamna ya nemi yafiyar ne a bainar jama’a inda kuma ya bukaci jam’iyyar ta tsayar da shi takarar gwamna a zaben 2023.
“Ina mai Allah wadai da jam’iyyar APC a Jihar Gombe domin sun tura ’yan daba sun tare mu a hanya sun fasa mana motoci guda hudu.
“Sannan sun kai hari gidan dan majalisar wakilai na tarayya Yaya Bauchi Tongo da ya bar APC ya koma PDP kwanan nan” in ji Jamilu.
Ya bukaci daukacin ‘ya’yan jam’iyyar da su dauki abin da ya faru a baya a matsayin kaddara.
Jamilu Gwamna, ya kara da cewa jama’a su yi hakuri tun da sun zabi jam’iyyar APC amma zaben ya zama zaben tumun-dare, ya bukaci mutanen Gombe su ba shi dama don ceto jihar.
Ya kara da cewa zabensa zai zama alkhairi in Allah Ya yarda saboda PDP ce ke da nasara tun da a bayyane kowa ya gaji da mulkin APC laakari da rashin walwala ga kuma tsadar rayuwa.
Ana iya tuna cewa, Jamilu Gwamna ya fice daga PDP bayan rasa kujerar takarar gwamnan Bauchi a 2019, inda ya koma APC lamarin da yamutsa hazo.
A ranar 2 ga watan Fabarairun wannan shekarar ne Jamilu Gwamna ya bar APC ya sake dawowa PDP.