Ana zargin wani mai mukamin Mataimakin Darakta a Gwamnatin Tarayya ya kashe kansa ta hanyar ratayewa bayan Hukumar EFCC ta gayyace shi zuwa ofishinta.
Rahotanni sun ce a ranar da Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arziki ta’annati ta bukaci jami’in Mataimakin Daraktan a Hukumar Bunkasa Makamashi na Zamani (NABDA) ya hallara a ofishinta da ke Abuja ne aka tsinci gawarsa.
- Yadda datse sadarwa ta shafi kasuwanci a Zamfara
- Kanzon kurege ne labarin datse sadarwa a Kaduna —El-Rufai
An tsinci gawar Christopher Orji, tana lilo ne a rataye a jikin fanka ne a gidanda da ke Rukunin Gidajen Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Abuja a ranar Litinin 30 ga Agusta, 2021.
Majiyoyi a hukumar ta NABDA sun ce ’yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike domin gano hakikanin musabbabin mutuwar mutumin.
Amma wani jami’i a NABDA ya ce babu yadda za a yi a ce mutumin ya kashe kansa, tunda bai bar wata takarda da ke nuna hakan ba a gidan.
Wakilinmu ya tuntubi mukaddashin mai magana da yawun hukumar ta NABDA, Nkiru Amakeze, amma ya ce ba shi da ta cewa.
“To me kake so in fada maka? Gaskiya yanzu ba zan iya cewa komai ba,” inji Amakaeze ga wakilin namu.
Kafin rasuwarsa, Mista Orji shi ne Shugaban Cibiyar Samar da Makamashin Zamani ta NABDA da ke Langtang a Jihar Filato.