Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Yobe (YSU), ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani saboda gwamnati ta kasa cika alƙawuran da ta ɗaukar musu.
Waɗannan alƙawura sun haɗa da ƙarin albashi, biyan bashin da suke bi, da kuma barin jami’ar ta riƙa gudanar da harkokinta da ƙashin kanta.
Shugaban ASUU na Jami’ar Yobe, Dokta Ahmed Karage, ya bayyana hakan bayan kammala wani taro da suka gudanar.
Ya ce sun fara yajin aikin ne bayan dogon lokaci da suka ɗauka suna tattaunawa da gwamnati, amma ba su cimma matsaya ba.
“Mun kwashe watanni muna magana da gwamnati, amma abin takaici shi ne dole ne yanzu mu tafi yajin aiki saboda gwamnati ta ƙi cika alƙawuran da ta ɗauka,” in ji Dokta Karage.
Daga cikin buƙatunsu akwai aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000, biyan bashin albashin da ya fara tun daga shekarar 2019, da kuma wasu haƙƙoƙinsu.
Ya ce jami’o’i su riƙa tafiyar da al’amuran su da kansu shi ne mafita don warware matsalolin da ake fama da su a fannin ilimi.
ASUU ta ce ba za su koma aiki ba har sai gwamnati ta magance matsalolin da suka gabatar.
Sun gargaɗi gwamnatin jihar kan ɗaukar matakin gaggawa don kaucewa kawo cikas ga kalandar karatu.
Har ila yau, ƙungiyar ta roƙi dalibai da su yi haƙuri, inda ta ce ta fara yajin aikin ba don cutar da su ba, illa dai domin neman haƙƙinsu da ya wajaba gwamnati ta biya.