Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil a Jihar Kano za ta hukunta dalibai maza 17 da suka yi wa wata daliba ihu don ta sanya rigar ‘Abaya’.
Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna wasu dalibai maza sun yi wa wata daliba da ke sanye da ‘Abaya’ kawanya suna mata ihun ‘Mai Abaya’.
- An cafke mai buga jabun kudi a wurin sayen rago
- El-Rufai ya sallami hadimansa 19
- An cafke mai yi wa Boko Haram safarar fetur
Shugaban Jami’ar, Farfesa Shehu Alhaji, ya tabbatar da fara bincike bayan samun rahoton tozarta dalibar da aka yi, ya kuma ce tuni aka gano wasu daga cikin daliban.
Ya ce Jami’ar ta kuma kafa kwamiti na musamman da zai binciki lamarin tare da gano hakikanin daliban da suka aikata hakan.
Idan ba a manta ba a watan Azumin Ramadana da ya gabata, Aminiya ta ruwaito yadda ’yan mata suka kirkiro gasar salon sanya Abaya a bikin karamar sallah a matsayin shigar yayi.
Sai dai kuma ’yan mata da dama sun guji sanya Abayar da sallar saboda gudun irin tozarcin da suka ga wasu mata da suka sanya ta suka fuskanta.
Masu sayar da rigar a wurare daban-daban sun samu ciniki sosai, inda aka dinga sayen ta kafin daga bisani a kawo cikas kan yayin.
A baya-bayan nan, a Kano Aminiya ta gano yadda matan da suka sanya Abaya ke fuskantar kabubale da cin zarafi daga samari.
Hakan ya kai wani yanayi da aka gano wata matashiya na sharbar kuka yayin da wasu samari ke mata ihu don ta sanya Abaya. Sai dai wasu dattijai sun cece ta daga ja’ircin samarin.
Amina Yusif, wata budurwa da ta sanya Abaya a lokacin bikin Karamar Sallah da ta gabata ta bayyana nadamarta saboda tozarcin da ta sha a hannun wasu matasa.
“Ka san yadda yawancin mata suke, ba su son abin da zai ja hankalin mutane gare su. Wannan shi ne abin da ya faru da ni da Sallah. Ban da na yi burus da lamarin da tuni na yi fada da wasu yara.
“Yanzu haka na mayar da Abayata can kasan kayana a cikin akwatina, ba zan sake sawa ba har sai an daina wannan abun,” in ji ta.