Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano ta ce za ta dauki sabbin dalibai 4,000 daga cikin 9,000 da ke neman gurbin karatu bayan sun ci jarabawar PUTME ta shekarar karatu ta 2020/2021.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Mukhtar Atiku-Kurawa ne ya bayyana haka a yayin da dalibai suke rubuta jarabawar a jami’ar a ranar Litinin.
- Pantami zai maka kafar da ta zarge shi da ta’addanci a kotu
- ’Yan bindiga sun kashe ’yan banga a kasuwa a Neja
- Ortom ya lashe amansa kan kisan sojoji 12 a Binuwai
“Akalla dalibai 11,000 ne suka zabi Jami’ar a matsayin zabinsu na farko amma 9,000 suka yi rijistar PUTME,’’ inji shi.
Ya ce, Jami’ar ta ware ranar Laraba 13, ga Afrilu, 2021 domin tantance dalibai masu neman gurbin shiga Jami’ar ta kai-tsaye (DE) su kimanin 2,000.
“Aikin tantance daliban zai ba wa Jami’ar damar fitar da daliban da za su yi karatu a makarantar.
“Adadin daliban da suka nuna sha’awar shiga Jami’ar Yusuf Maitama Sule, ya zarta wanda Hukumar Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta amince wa Jami’ar,’’ kamar yadda ya bayyana.
Rahotanni na cewa Jami’ar ta dauki dukkan matakan da suka kamata na yaki da cutar COVID-19 a lokacin jarabawar ta PUTME.