✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’ar Jihar Gombe ta janye daga yajin aikin ASUU

Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Jihar Gombe ta ummarci daukacin malaman jami’ar da su koma bakin aiki ba tare da bata lokaci ba. Ummarnin na kunshe…

Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Jihar Gombe ta ummarci daukacin malaman jami’ar da su koma bakin aiki ba tare da bata lokaci ba.

Ummarnin na kunshe ne a ciki wata sanarwa da magatardar jami’ar, Dokta Abubakar Aliyu Bafeto ya sanya wa hannu a safiyar Juma’a 2 ga watan Satumba, 2022.

Sanarwar ta ce, hukumar gudanarwara Jami’ar ta cimma wannan matsaye ne a wani taron gaggawa da manayan jami’anta suka yi ranar Alhamis.

Dakta Bafeto a cikin sanarwar ya ci gaba da cewa, hukumar jami’ar za ta dauki matakin kin biyan albashi ga duk malamin da ya ki komawa bakin aikinsa daga zuwa ranar 9 ga watan Satumba.

Dangane da haka, jami’ar ta tanadi rajista da kowanne malami zai sa hannu a ofisoshin shugabannin kowanne sashe da bangare ga malaman da ke son dawowa bakin aiki.

Wakilimu ya bayar da rahoton cewa hukumar jami’ar ta fara gudanar da karatu ga sabbin dalibai tun ranar 22 ga watan Agusta, kuma ta shirya yin bikin rantsar da sabbin dalibai a ranar Asabar, 3 ga watan Satumba.