Ana fargabar cewa wata daliba ta kashe jaririn da ta haifa a Jami’ar Jihar Gombe a wannan Asabar din.
Dalibar ’yar aji hudu ce da ke sashin koyar da gudanar da harkokin al’umma wato Public Administration, wacce bayan ta haihu ta jefar da jaririn ta taga kuma hakan ya yi sanadiyar fashewar kansa har ya mutu.
- Gwamnati za ta gina gidaje 1,000 a jihohin Arewa 7 — Shettima
- Girgizar Kasa: Mutanen da suka mutu a Morocco sun zarta 1,000
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta a jami’ar ta shaida wa Aminiya cewa dalibar ta haihu ne ba tare da ta yi aure ba.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, dalibar ta haihu ne da misalin karfe 7 zuwa 8 na safiyar wannan Asabar din a daya daga cikin bandakunan da ke rukunin dakunan kwanan daliba, sannan ta jefar da jaririn ta taga.
A cewar majiyar, bayan gudanar da bincike an kama dalibar kuma aka damka ta a hannun hukumar jami’ar inda aka soma tabbatar da koshin lafiyarta a asibiti sannan aka mika ta a hannun iyayen ta.
Wakilinmu da ya tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Gombe, ASP Mahid Mu’azu Abubakar domin jin ta bakinsa kan lamarin, ya shaida masa cewa har zuwa wannan lokacin da bai samu labarin ba amma zai bincika domin jin yadda ta kaya.