Jami’ar Benin ta ce za ta hada gwiwa da Cibiyar Binciken Makamin Nukiliya ta Turai (CERN) domin fara bincike a fannin kimiyya da fasahar Nukiliyar a Najeriya.
Sashen yada labarai na jami’ar ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
- ’Yan Sanda na binciken dalilin mutuwar matasa 21 a gidan giya a Afirka ta Kudu
- ’Yan bindiga sun fara harbin fasinjojin jirgin kasan da ke hannunsu
Sanarwar ta ce wasu daliban makarantar su biyu, Decent Oghifo da David Dosu da a kwanakin baya suka sami nasarar tsallake tantancewar da cibiyar ta CERN za su je hedkwatarta da ke Geneva domin daukar wani kwas da ta shirya.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, wannan ne karo na farko da dalibai daga yankin Kudu da hamadar Sahara suka sami matsuguni a shirin.
Jami’ar ta kuma ce Daraktan sashen bincike da Ci gaban Jami’ar, Farfesa Musibau Bamikole, ya gabatar da daliban ga Shugaban Jami’ar Farfesa Lilian Salami, da kuma sauran shugabnnin gudanarwarta.
A nasa bangaren, Shugaban jami’ar ya bayyana farin cikinsa kan wannan nasara da daliban da ma jami’ar suka samu, tare da ayyana hadin guiwar jami’ar da cibiyar CERN a matsayin babban ci gaba da zai sake daga darajar jami’ar a Najeriya da idon duniya.