✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’ar Benin Ta Karyata batun janye yajin aiki

Jami'ar ta ce har zuwa yanzu jami'ar ba ta sanya ranar komawa aiki ba.

Hukumar gudanarwar Jami’ar Benin ta musanta labarin da ake yadawa cewa za ta koma bakin aiki a ranar 20-ga oktoban 2022.

Jita-jitar dai ta fara yawo ne mako biyu bayan jami’ar ta saki sakamkaon daliban da suka rubuta jarabawar shiga jami’ar ta Oost UTME da Direct Entry.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin mai dauke da sa hannun kakakinta, Benedicta Ehanire, jami’ar ta shawarci daliban da ma iyaye da sauran al’umma, da su yi watsi da jita-jitar.

Haka kuma ta ce har zuwa yanzu jami’ar ba ta sanya ranar komawa aiki ba.