✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Azman da wasu 36 sun samu lasisin fara aiki

Hukumar NUC tana damka wa Jami'ar Azman da Jiami'ar El-Amin da ke Minna a Jihar Neja da sauran 35 lasisinsu ne a Abuja

Jami’ar Azman mai zaman kanta da aka kafa a Jihar Kano da wasu sabbin jami’o’i masu zaman kansu a Najeriya na karbar lasisinsu na fara aiki a ranar Juma’a

Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) na damka wa Jami’ar Azman da Jiami’ar El-Amin da ke Minna a Jihar Neja da sauran 35 lasisinsu ne a hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Shugaban Kwamitin Amintattu na Jami’ar El-Amin, mallakin kamfanin El-Amin Nigeria Limited, shi ne tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Takwaransa na Jami’ar Azman kuma shi ne Barista Ado Muhammad Ma’aji, kuma jami’ar mallakin Rukunin Kamfanin Azman ce.

Kamfanin Azman ya fara ne da harkar man fetur daga baya ya shiga harkar sufurin jiragen sama kafin yanzu su fara harkar jami’a.