Kamfanin sufurin jiragen sama na Azman ya dawo da zirga-zirga a filin jirgin saman kasa da kasa na Kaduna, bayan ya shafe tsawon wata biyu da dakatar da aiki saboda hare-haren ta’addanci a kusa da shi.
Jirgin farko na kamfanin dai ya sauka a filin jirgin ne wajen misalin 12:00 na ranar Litinin.
- Bayan rasa tikitin takara, dan Namadi Sambo ya bukaci wakilan zabe su dawo masa da kudinsa
- Jami’an EFCC sun yi wa gidan Okorocha kawanya
Tun a ranar 28 ga watan Maris ce dai kamfanin ya dakatar da zirga-zirga a filin bayan ’yan bindiga sun kai hari cikinsa, inda har suka kashe wani ma’aikacin filin.
Kwana daya da kai harin ne kuma ’yan bindiga suka kai wa jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja hari, suka kashe mutum 10 sannan suke ci gaba da tsare mutum 61 har zuwa yau.
Sai dai an dan fara samun sauki bayan daya daga cikin kamfanonin ya dawo da aiki.
Jirgin na Azman dai ya sauka ne da fasinjoji 42, inda wasu daga cikinsu suka biya sama da N100,000 kudin tikiti daga Abuja zuwa Kaduna.
Tafiyar Abuja zuwa Kaduna dai ba ta wuce ta minti 20 ba a jirgi.
Kodayake jirgin ba kai tsaye ya sauka a Kadunan ba, sai da ya biya ya sauke fasinjojin Legas kafin ya sake debo su zuwa Kaduna.
“Hakan na nuni da yadda mutane suka damu da yin tafiyar daga Abuja zuwa Kaduna, sakamakon dakatar da sufurin jirgin kasa a hanyar,” a cewar wata majiya.
Wani ma’aikacin kamfanin na Azman wanda ya tabbatar da dawowar zirga-zirgar jiragen ga Aminiya ya ce jirgin zai rika sintirin ne da fashin kwana dai-daya, inda jirgi na gaba zai sake sauka ranar Laraba.
Kamfanin dai ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Wannan wani lokaci ne mai cike da tarihi ga masu sufurin jiragen sama inda aka sake bude filin bayan an rufe shi tsawon wata biyu. Abin farin ciki ne.”