Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta dakatar da kamfanin AZMAN saboda rike mata Naira biliyan 1.2.
NCAA ta dauki matakin ne ’yan makonni bayan ta yi barazanar rufe harkokin AZMAN saboda kin biyan bashin wasu Naira biliyan biyu da kuma Dala miliyan 7.8 daga kudin sayar da tikiti da kuma jigilar kaya (TSC/CSC).
Aminiya ta gano cewa kamfanin Jiragen Sama na AZMAN ya dakatar da harkokinsa na jigila a ranar Alhamis bayan NCAA ta ki sabunta lasisinsa na daukar fasinja (ATL).
Wajibi ne kamfanin jirgin sama ya mallaki lasisin ATL, wanda ake sabuntawa lokaci zuwa lokaci, kafin ya samu izinin yin aiki.
Abin da ya hada mu —NCAA
Darakta-Janar na NCAA ya ce, “Wannan ba cajin su muka yi ba, ba kuma kudinsu ba ne, kudadenmu ne da muka wakilta su su karba mana daga fasinjoji, amma suka kashe.
“Ba tara ko kudin ruwa muke bukata su biya ba, so kawai muke su ba mu kudadenmu.
“Na gaji da yi wa minista da Akanta-Janar na Kasa da Fadar Shugaban Ƙasa bayani kan rashin bai wa gwamnati kudadenta. Dole ce ta sa muka dauki wannan mataki.” in ji shi.
Aminiya ta gano akwai yiwuwar a cikin ’yan kwanaki masu zuwa NCAA ta dauki irin wannan mataki a kan karin kamfanonin jiragen sama.
TSC/CSC da amfaninsa
TSC/CSC haraji ne da kowane fasinja ke biya a lokacin sayen tikitin jirgin sama, wanda gwamnati ke karba ta hannun NCAA daga kamfanonin da suka sayar da tikitin.
Bayan karbar kudaden ana rabawa ne ga hukumomi biyar na bangaren jiragen sama.
Hukumomi da ake raba wa TSC/CSC su ne NCAA, Hukumar Kula da Sararin Samaniya (NAMA), Hukumar Binciken Yanayi ta Kasa (NiMET), Hukumar Binciken Hatsari (AIB) da kuma Kwalejin Tukin Jirgin Sama (NCAT), da ke Zariya.
A bisa doka, NCAA ke samun kashi 58 cikin wani 100 na kudaden, a matsayin kashi 70 cikin 100 na kudadan gudanarwarta; ragowar hukumomin kuma ake raba musu kashi 42 cikin wani 100 na TSC/CSC din da ya rage.
Darakta-Janar din NCAA ya bayyana cewa ba lasisin aikin AZMAN (AOC) aka kwace ba, kuma kamfanin ya mika musu tsarin yadda yake son biyan kudaden, amma hukumar ba ta gamsu da tayin ba.
Ya ce, “Biliyan N1.2 muke bin su na TSC/CSC, amma da muka kira su aka kafa kwamiti a kai sai suka ce za su rika biyan miliyan N10 a duk wata, amma ba mu amince ba.
“Daga baya suka kara zuwa miliyan N20, mu kuma muka ce dole sai miliyan N50.
“Da mun amsa N10m din, to da sai nan da shekara 12 kafin su gama biyan kudadenmu da muka wakilta su su karba mana, wannan ai asara ce.”
Mun biya kudaden —AZMAN
Amma a hirasa da wakilinnmu, Janar-Manaja na Azman, Suleiman Lawal, ya ba da tabbacin cewa kamfanin zai ci gaba da gudanar da ayyukansa a ranar Juma’a, yana mai bai wa abokan hulda hakuri bisa tsaiko da aka samu.
Ya ce, “An samu matsala ce ta fuskar sadarwa, amma jiragenmu za su ci gaba da aiki.
“Mun biya komai, matsalar sadarwa kawai aka samu, amma gobe (Juma’a)maza mu ci gaba da aiki.
Daga: Sagir Kano Saleh, Absullateef Aliyu (Legas), Salim Umar Ibrahim (Kano).