Jami’ar East Carolina (ECU) dake kasar Amurka wacce a kwanaki aka rawaito na nada Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin farfesa ta ce ba ta da masaniya a kan nadin.
A cikin wata wasika da ta aikewa gwamnan, jami’ar ta ce sanarwar nadin wacce aka alakanta da daya daga cikin mambobin tsagayoyinta ba ta sami sahalewar hukumar gudanarwarta ba, hasali ma ba ta san da ita ba.
- Majalisar Kano ta amince Ganduje ya karbo bashin N20bn
- Zaben Kananan Hukumomi: Rikici ya barke a jam’iyyar APC reshen Kano
Hakan dai na zuwa ne kasa da mako daya bayan Gwamna Ganduje ta bakin mai magana da yawunsa, Abba Anwar ya yi ikirarin cewa Tsangayar Fasahar Sadarwa ta Kasa da Kasa ta Jami’ar ta nada gwanman a matsayin babban malami kuma farfesa a fagen shugabancin kasa da kasa.
Sai dai Jami’ar a cikin wasikar ta nesanta kanta daga wasikar wacce aka aike masa da ita ranar 30 ga watan Nuwamban 2020.
Ta ce, “Muna sanar da kai cewa wasikar da ka karba daga Dakta Victor Mbarika ranar 30 ga watan Nuwamba ba ta da sahalewar jami’armu.”
Wasikar, wacce take dauke da sa hannun shugaban makarantar, Grant B. Hayes ta ce shi kadai ko mataimakin shugabanta ko kuma daya daga cikin wadanda aka wallafa sunansu a jikinta ne kadai ke da damar tabbatarwa da wani irin wanna mukamin.
A cewarta, Dakta Victor ba ya daya daga cikin masu wannan hurumin a jami’ar.
A kwanakin baya Abba Anwar ya ce ECU ta nada mai gidan nasa bayan gamsuwarta da irin nasarorin da ya samu a bangaren kyakkyawan shugabancinsa da kuma jajircewarsa wajen gina dan Adam a jihar Kano.
“Muna taya ka murna, gamayyar malaman Tsangayar Fasahar Sadarwa ta Jami’armu na farin cikin sanar da kai cewa an nada ka a matsayin babban malami kuma farfesa a fannin shugabancin kasa da kasa,” inji sanarwar da Abba ya fitar a ranar Talata.
Ya kuma ce jami’ar ta yanke shawarar nada shi ne la’akari da irin tarin ilimin da yake da shi domin amfana da shi wajen rayawa da ci gaban kasa.