Cibiyar Bincike kan Harkokin Noma (IAR) ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta kirkiro wani sabon nau’in takin zamani domin bunkasa samar da abinci a kasa.
Babban Daraktan cibiyar, Farfesa Muhammad Faguji Ishaku, ne ya bayyana haka lokacin bikin nuna wa manoma takin da aka gudanar a garuruwan Maigana da Pampaida da ke Kananan Hukumomin Soba da Ikara a Jihar Kaduna.
- Farashin man fetur zai iya kaiwa N340 a 2022 – NNPC
- Abin da ya sa muka ragargaza babura 482 – Gwamnatin Legas
Farfesan ya ce cibiyar ta gudanar da bincike akan takin ne da hadin gwiwar wata kungiya mai rajin habaka aikin gona watau, AGRA, kuma za a iya sanya wa masara da shinkafa da kuma waken soya.
Ya ce an gudanar da binciken ne ta hanyar kimiyya kuma aka gayyaci manoma kasancewar sune masu amfana da duk wani nau’in bincike da cibiyar take gudanarwa.
Ya kara da cewa aikin binciken kokari ne na Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta tarayya, yayin da ita kuma cibiyar ta samar da kwararrun da suka gudanar da binciken.
Babban Daraktan ya kara da cewa aikin ya hada da bangarori masu zaman kansu kamar kungiyar masu sarrafa takin zamani da saidawa.
A cewarsa burin cibiyar shi ne ganin manoma sun rungumi sabon takin zamanin domin habaka amfanin gonarsu.
Farfesa Faguji, ya ce lokaci ya yi da za a samar wa kowane irin hatsi nashi nau’in takin zamanin da ya kunshi duk irin sinadaran da ya kamata domin manoma su rinka samun gwaggwabar riba.
Shima a nasa jawabin, shugaban tawagar wadanda suka gudanar da binciken a cibiyar, Farfesa Bitrus Tarfa, ya ce tuni binciken ya kai kololuwar da ake bukata kasancewar tuni aka samar da takin da manoma za su sanya wa amfanin nasu.
Ya ce an gudanar da binciken ne da tallafin Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Jihar Kaduna.