✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’ar Abuja ta daga likafar Malamai 10 zuwa matsayin Furofesa

Majalisar da ke sa ido kan al’amuran gudanarwa a jami’ar Abuja, ta amince da yi wa malamanta 10 karin girma zuwa matsayin furofesa. Hakan na…

Majalisar da ke sa ido kan al’amuran gudanarwa a jami’ar Abuja, ta amince da yi wa malamanta 10 karin girma zuwa matsayin furofesa.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar mai dauke da sa hannun Dokta Habib Yakoob, shugaban sashen yada labarai da hulda da al’umma na jami’ar ya fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa ba da lamunin yin karin girman ya biyo bayan tantance lakcarorin da abin ya shafa yayin zaman Majalisar Gudanarwa na Jami’ar karo na 87 da aka gudanar a baya bayan nan.

Dokta Yakoob ya ce, bayanan tantancewar sun nuna cewa an daga matsayin malamai 6 zuwa matakin furofesa, yayin da ragowar 4 aka daga likafarsu zuwa matsayin na kusa da furofesa wato associate professor.

A cewarsa, malaman da suka zama Furofesoshi sun hada da Dokta Wasiu Olugbeng Gabadeen; Dokta Ogbe Adamu Okuwa; Dokta Idu Ejoga; Dokta Pam Z. Chuwang; Dokta Binta Ibrahim Zaifada da Dokta Oke Eunice Bose.

Ya kuma jeranto sunayen wanda aka ba mukamin na kusa da furofesa da suka hadar da; Dokta Hamza Na’Uzo, Dokta Wada Mathew Sunday, Dokta Biyaya Beatrice da kuma Dokta Yunusa Thairu.

Shugaban jami’ar Farfesa Abdul-Rasheed Na’Allah, a cikin sakonsa na taya murna, ya ce malaman sun samu karin girma a sakamakon kwazon da suka yi a fagen nazari da binciken ilimi.