✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Daya daga cikin masu fasa banki da shaguna a Legas ya shiga hannu

Rahotanni sun tabbatar da kama daya daga cikin wadanda ake zargin sun fasa banki da manyan shaguna dake yankin Lekki a jihar Legas bayan zanga-zangar…

Rahotanni sun tabbatar da kama daya daga cikin wadanda ake zargin sun fasa banki da manyan shaguna dake yankin Lekki a jihar Legas bayan zanga-zangar da ta rikide zuwa tarzoma a ranar Talata.

Na’urar CCTV ce dai ta dauki hoton wanda ake zargin a lokacin da yake tsaka da kwasar kudade da kayyaki a cikin wani rumbun ajiyar kudi dake wani babban shago.

Majiyarmu ta ce da yawa daga cikin wadanda suka aikata laifin na’urar CCTV ta dauki hotunansu, kuma jami’an ‘yan sanda na ci gaba da bincike akansu domin a kama su.

“An sami nasarar cafke daya daga cikin wanda suka fasa banki da wasu manyan shaguna a yankin Lekki kuma kuma an same shi da kudade da yawa, ragowar ma ana kan farautarsu yanzu haka,” inji majiyar tamu.

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai Rundunar ‘Yan Sanda Ta jihar Legas ba ta tabbatar da lamarin ba.

Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi bai daga wayar da aka kira shi ba domin jin martaninsu kan lamarin.