Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta fara farautar wani fitaccen mai sayar da muggan kwayoyi da ke Lekki a Jihar Legas wanda ya kade jami’inta da mota.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Mista Femi Babafemi ya fitar a ranar Laraba a Abuja, ta ce wanda ake zargin, Sowunmi Ayodeji-Kayode, ya buge jami’in da gangan kokarinsa na tserewa.
Babafemi ya ce a ranar 18 ga watan Agusta jami’an hukumar suka kai samame gidan wani dillalin da ake nema ruwa a jallo da ke lamba 2/3 Adetola Ayeni kusa da Lekki, a Legas, bayan wasu bayanan sirri da suka samu cewa yana fataucin miyagun kwayoyi a gidan.
“Duk da cewa ba ya gidan a lokacin da jami’an tsaro suka shiga, amma ya dawo yayin da ake tsaka da bincike a gidansa.
“Yayin da ya hango jami’an NDLEA, sai ya juya motarsa nan take kuma ya buge jami’i daya.
“Yayin tserewa ya rusa katangar makwabcinsa kuma daga nan ya tsere.
“Binciken da aka yi a gidansa ya kai ga gano kilo 10.5 na wata kwaya sannan an samu sauran miyagun kwayoyi a gidan.”
Babafemi ya rawaito shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa ya bada umarnin tura jami’an tsaro don nemo wanda ake nema ruwa a jallo.
Marwa ya ba da umarnin yi wa jami’in da aka buge da mota magani.