Wata kwambar jami’an tsaro na DSS da NSCDC, gami da ma’aiktan Babban Banki Najeriya (CBN) sun kai sumame kan masu sayar da sabbin kudi a Kano.
Rundunar tsaro ta Sibil difens, ta ce ta kai samamen ne a Central Otal da ke birnin, a inda suka kama mutane 14 masu sana’ar, ciki har da wata mace.
- Mun daina kai wa CBN ajiyar kayan zabe —INEC
- Gwamnan CBN ya sayi fom din Takarar Shugaban Kasa a APC
Shugaban Hukumar tsaron na jihar Kano Adamu Zakari ya ce, kamen masu cinikin kudin ya zama dole saboda sana’ar da su ke yi, ya ci karo da sashe na 20 na dokar babban Bankin Najeriya.
Sashen da ya haramta saye da sayar da kudi da yin jabunsa da kuma tallar sa, wanda ya hada da takardun kudin da kuma sulalla da makamantansu ne ya jagoranci aikin.
Sannnan ya ce laifi ne: “Liki da kuma watsa kudi da jama’a ke yi a bukuwa da rubutu a jikin takardun kudin da dukunkuna su, gami da yin jabunsu duk laifi ne, da ka iya janyo hukunci a bisa doka.”
Rundunar tsaron ta baje kolin mutanen 14 da ta kama a sumamen a harabar ofishinta da ke Kano, ta kuma bayar da sunayensu kamar haka:
Wadanda aka kama suna sayar bandirin N5000 ne, ’yan 50, a kan N7,000 ne, yawanci ga masu zuwa shagalin biki inda ake lika wa makada da masu rawa.