Gwamnatin Najeriya ta ce jami’an tsaron da ke kare gidan yarin Kuje a birnin Abuja, sun yi iyakacin kokarinsu wajen dakile harin da ’yan ta’adda suka kai, amma abin yafi karfinsu, saboda yawan maharan da kuma manyan makamansu.
Ministan Kula da Harkokin ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Maigari Dingyadi ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, jim kadan bayan kammala taron gaggawa na Majalisar Tsaron Kasa da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Fadar Shugabancin Kasar da ke Abuja.
Dingyadi ya kuma bayyana cewa, shugaban Buhari ya umarci hafsoshin tsaro da su tabbatar da daukar kwararan matakan da suka dace bayan gudanar da bincike kan musabbabin faruwar lamarin, domin hana maimaituwarsa.
Tuni dai kungiyar ISWAP wato tsagin da ya balle daga Boko Haram mai biyayya ga IS, ta dauki alhakin harin da gungun ‘yan bindiga suka kai gidan yarin Kuje da ke Abuja, babban birnin Najeriya, wanda ya kai ga tserewar daruruwan masu laifi.
Wani hoton bidiyo da kungiyar ta fitar a ranar Laraba mai dakika 38, ya nuna yadda mayakanta su ke shiga gidan yarin bayan fasa kofarsa da suka yi a daren ranar Talata.
Yayin ziyarar da ya kai gidan yarin bayan harin da aka kai, Ministan Tsaron Najeriya, Bashir Salihi Magashi, ya ce babu fursuna dan Boko Haram da ya rage a tsare a gidan gyaran halin.
Magashi ya ce gidan yarin na daukar adadin fursunonin da yawansu ya kai 994, kuma alkaluma sun nuna cewar fiye da 600 daga cikinsu ne suka tsere a lokacin harin da ‘yan ta’addan suka kai, kuma akwai mayakan Boko Haram kimanin 64 a cikinsu.
Tuni dai Hukumar Kula da Gidajen Gyara Hali a Najeriya (NCS), ta fitar da sunaye da hotunan wadanda ake zargin ’yan ta’addan kungiyar Boko Haram ne da suka tsere daga gidan yarin na Kuje.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, hukumar ta ayyana mayakan kungiyar 69 a matsayin wadanda take nemansu ruwa a jallo.