✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 10 a Zamfara

’Yan bindigar sun kai wa jama’a farmaki a yankin Mada na kauyen Hayin Daudu.

Rundunar hadin gwiwa ta jami’an ’yan sanda da ’yan banga a Jihar Zamfara, ta yi nasarar kashe ’yan bindiga 10 a kauyen Hayin Daudu da ke Gusau, babban birnin Jihar.

Kakakin ’yan sandan Jihar, SP Muhammad Shehu ne ya inganta rahoton yayin zantawarsa da wakilinmu a ranar Litinin.

A cewarsa, ’yan bindigar sun kai wa jama’a farmaki ne a yankin Mada a kauyen Hayin Daudu.

“Amma da samun rahoton shigarsu yankin, hadin gwiwar jami’an tsaron suka kai dauki tare da tarwatsa su wanda a dalilin artabun da aka yi, jami’an tsaron suka kashe 10 daga cikin ’yan bindigar.

“Tuni al’amura suka koma daidai a yankin kuma jami’an tsaro sun daura damarar zama cikin shirin ko ta kwana domin dakile aukuwar wani harin a gaba,” a cewarsa.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Mista Hussaini Rabi’u, ya jinjina wa jami’an tsaro dangane da bajintar da suka nuna wajen tunkarar ’yan bindigar yayin da suka kai harin.