Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga da dama a yayin wani samame da suka kai a kananan hukumomin Igabi da Chikun a Jihar Kaduna.
Kazalika, jami’an tsaron sun yi nasarar cafke wani malami, Malam Idris Audu, tare da matar fitaccen dan bindigar nan Zubairu, wato Rabi Hajiya Karime.
- Buhari ya ce ko an kara mishi wa’adin mulki ba zai karba ba
- Ban taba cin bashi ba a lokacin da nake gwamna —Kwankwaso
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
Ya kara da cewar jami’an tsaro sun cafke wasu mutum biyu da ake zargin suna hada baki da ’yan bindiga.
A cewar Aruwan, an kai samamen ne a yankin Faka, Katuka, Barebari da Maguzawa, wadanda suke karkashin kananan hukumomin Chikun da Ighabi a Jihar.
Ya kara da cewa an hangi gawarwakin ’yan bindiga da dama a kogin Maguzawa, bayan dakarun sojin sama sun yi musu luguden wuta da jiragen yaki.
Har wa yau, ya ce jami’an tsaro sun kai samame yankin Katuka mai nisan kilomita tara da Kangon Kadi a Karamar Hukumar Chikun, inda a nan kuma suka cafke wani dan bindiga.
Daga cikin makaman da aka samu daga hannun ’yan bindigar akwai bindiga kirar AK47, harsasai, miyagun kwayoyi.
Ya ce Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya nuna jin dadinsa kan nasarar da jami’an tsaron suka samu a yayin samamen.