✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’an tsaro sun ba da belin Ali Baba bayan kalamansa a kan Kwankwaso

Jami’an tsaro sun bayar da belin mai bai wa gwamnan Kano shawara a kan harkokin addini, Ali Baba biyo bayan cafke shi da suka yi…

Jami’an tsaro sun bayar da belin mai bai wa gwamnan Kano shawara a kan harkokin addini, Ali Baba biyo bayan cafke shi da suka yi saboda wasu kalamai da ya yi game da kamfanin ‘Aliko Oil’.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana wa Aminiya cewa, jami’an tsaro sun ba da belinsa bisa sharadin janye kalaman nasa da ya yi.

Ali Baba ya yi wasu kalamai ne, inda yace gidan Man Aliko da ke Kano da wasu sassa na kasar nan mallakar tsohon gwamnan jihar ne, Rabiu Musa Kwankwaso.

Ali Baba ya yi wannan kalamai ne a wata hira da aka yi da shi a cikin wani shirin na musamman da gidan rediyon Express da ke Kano ya dauki nauyi.

Aminiya ta ruwaito cewa Kamfanin na ‘Aliko Oil’ bai yi ammana da kalaman na Ali Baba ba, wanda nan take ya maka shi a kotu domin neman ya bada hujja a kan furucin da ya yi.

Sai dai hadimin Gwamnan ya amince tare da rubuta takardar janye kalaman nasa, kafin daga bisani aka bayar da belinsa.