Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana ganin jami’an tsaro ba sa yin abin da ya dace, idan aka kwatanta da irin abubuwan da aka samar musu.
Buhari, a cewar Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Babagana Monguno, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin taron Majalisar Tsaro ta Kasa da aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
- Sojoji sun kwace bindigogi 517 a Filato da Kaduna
- Dalilin da jirgin soja ya kashe kananan yara a Neja —Gwamnati
Ya ce shugaban ya bayyana bakin cikinsa kan kashe-kashen da ake yi a baya-bayan nan da kuma sace wasu ’yan Najeriya da ’yan bindiga ke yi.
Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan kammala taron, Monguno ya ce Buhari ya yi bakin ciki saboda hare-haren da jami’an tsaro suka kasa kawo karshensu.
Ya ba da misali da harin da aka kai kan jirgin Abuja zuwa Kaduna wanda ya yi sanadin mutuwar wasu fasinjoji tare da yin garkuwa da wasu.
Monguno ya ce Buhari kadai ba zai iya daukar nauyin matsalar rashin tsaro a kasar gaba daya ba saboda nasa bangaren shi ne yanke shawarwari masu inganci wanda a halin yanzu yake yi.
Ya ce shugaban ya umurci dukkan shugabannin hukumomin tsaro da su tabbatar da sako duk wadanda aka sace a fadin kasar nan.
Ya ce Buhari ya kuma umarci dukkanin jami’an tsaro da na tara bayanan sirri da su gaggauta kubutar da duk mutanen da aka yi garkuwa da su cikin aminci, ciki har da fasinjojin jirgin kasa da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su.
Monguno ya ce Buhari na duba rahoton da ya mika mishi, mai dauke da shawarwari masu yawa kan matakin tsaro a kan iyakokin kasa da kuma cikin kasar.
Ya ce mai yiwuwa shugaban ya sake kiran wani taro nan gaba kadan bayan ya yanke shawara kan ratohon da ya shafi halin da ake ciki halin da hukumomin tsaro suke ciki da kuma bukatunsu da kalubalen da suke fuskanta.
Monguno jaddada bukatar samun bayanan sirri na dan Adam tare da gargadin cewa matsalar tsaro na iya dawwama fiye da wa’adin da ake sa ran zai kawo karshe idan al’umma ta ki bayar da bayanan da ake bukata domin tada zaune tsaye.