✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an Kwastam sun kama buhuna macizai

Jami’an kwastan a makon jiya a Kalaba Jihar Kuros Riba suka kama kwantena uku makare da buhunan macizai da sauran kwari buhu 140, wadanda aka…

Jami’an kwastan a makon jiya a Kalaba Jihar Kuros Riba suka kama kwantena uku makare da buhunan macizai da sauran kwari buhu 140, wadanda aka shigo da su Najeriya ta ruwa daga kasar Kamaru.

Sauran kwarin da Aminiya,  ta samu labarin an shigo da su ta ruwa sun hada da shanshani, kwadi samfurin burduddigi, gizo-gizo da aka shigo da su kasar nan domin sayarwa  ko kiwo da kuma sauran bukatu an kiyasta kudinsu da kimanin Naira milyan shida da rabi.  

Da yake yi wa manema labarai karin bayani game da kamen da suka yi a gabar ruwan Kalaba, kwamandan shiyar jami’an kwastan mai kula da Kuros Riba da Akwa Ibom  Misis Nanbyen Burromyyat ta ce jam’anta ne da ke aikin sintiri suka kama kayan, inda ta bayyana cewa, ‘kayan da aka kama sun saba wa doka sashe na 3 da ta haramta safara da kuma fataucin irin wadannan halittu.

A cewar Kwaturolar, ‘saboda tsoron ka da halittun a budesu domin a gani su fito wasu su tsere ne ya sanya ta ki amincewa da a yi hakan, amma fa ta ce ta mika masu laifin da ake zargi da kayansu ga hukumar aikan gona da kebe halittu da kwari, domin su  tantance kwarin.   Kuma  za su ci gaba da bincike a kansu. 

Hukumar har wayau ta ce tun ranar 24 ga watan Yuli ne aka shigo da kayan, wadanda hukumarsu ta yi sa’ar kamawa.

Babbar jami’ar kwastan din har wa yau da aka tambayeta ko me take ji za a yi da wadancan  da su? Ta ce Allah ya huwace wa kasar nan nau’in macizai da ba sai wani ya je wata kasa ya shigo da su ba.  Sai dai daya daga cikin masu kayan da ya shigo da su daga Jamhuriyar Kamaru mai suna Julius Yoyigana ya shaida wa Aminiya cewa shi bai san abin da buhunan suka kunsa ba.

“Abokina ne ya ba ni ya ce ga sako nan in kai wa wani amininsa a Legas abin da nake da shi lambar wayar wanda zai karbi kaya da na buga masa waya sai ya ce in jira shi a nan Kalaba, akwai wani wanda zai zo ya karbi kayan a hannuna,” inji shi.

Shi kuwa direban jirgin ruwan da ya kawo buhunan macizai Najeriya,, bictor Agbor, ya gaya wa ’yan jarida cewa ba su kula da kunshin kayan ba a cikin jirgin kafin su taso daga Kamaru zuwa nan Najeriya sai da muka shigo Najeriya ne aka sanar da ni cewa akwai kayan a cikin jirgi na.inji Agbor direban daga kamaru.