✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’an JAMB na hada baki a yi fashin takardar jarabawa

Ma’aikata na hada baki a yi fashi domin samun takardar jarabwar JAMB.

Magudin jarabawar shiga manyan makarantu ta JAMB ta dauki sabon salo, inda ma’aikatan Hukumar ke hada baki a yi fashi domin samun takardar jarabawar.

Shugaban Hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ya ce duk da kokarin JAMB na fitar da sabbin hanyoyin hana satar jarabawa, wasu “mutane na ganin suna da wayo” za su iya murde tsarin.

Ya ce, “Abin ya kai ga ana hada baki da ma’aikatan wuci gadi da ma cikakkun ma’aikatanmu su ce an yi musu fashi, an sace madaukin tambayoyin ko an yi musu musanyarsa.”

Farfesa Oloyede, ya koka da cewa abin takaici ne yadda ma’aikatan da hukumar ta ke dauka aikin jarabawa suka rungumi mummunar dabi’ar.

Amma a cewarsa, Hukumar na daidai da ta fallasa duk masu satar jarabawa, ta kuma tabbatar da cewa sun fuskanci hukunci.

“Mu dai abin da muke cewa shi ne duk wanda zai kawo mana matsala a wurin gudanar da aikinmu, ba za mu raga masa ba,” inji shi.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin da yake zagaje domin ganin yadda jarabawar JAMB ta UTME ta bana ke gudana a yankin Kudu maso Gabas.

Sai dai ya bayyana wa manema labarai cewa salon satar jarabar a yankin Arewa ta dan sha bamban da yadda ake yi a yankin Kudancin Najeraiya.