✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an Hisbah sun cafke matasan da ke buga karta a Kano

Hukumar dai ta yanke musu hukuncin karanta Alkur'ani.

Jami’an hukumar Hisbah a Jihar Kano sun cafke wasu matasan da aka samu suna buga wasan karta a Karamar Hukumar Warawa da ke Jihar.

An dai kama matasan ne a garin na Warawa bisa zarginsu da bata lokacinsu a banza, a maimakon su yi amfani da shi ta wani abin da zai amfanmi rayuwarsu.

Hakan ne ya sa jami’an hukumar suka raba musu takardun Alkur’ani sannan suka umarcesu da su karanta a matsayin hukunci.

Matasan kenan lokacin da suke karanta Alkur'ani
Matasan kenan lokacin da suke karanta Alkur’ani

A cikin wata gajeruwar sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook, Hisbah ta ce, “Ofishin hukumarmu da ke Karamar Hukumar Warawa, karkashin Babban Kwamnadan hukumar, Dokta Harun Sani Ibn Sina, ya kama wasu matasa saboda bata lokacinsu wajen buga wasan karta.

“Daga nan ne ofishin ya raba musu wani bangare na Alkur’ani tare da umartarsu da su karanta don su ribaci lokacin nasu,” inji hukumar.

A yan watannin nan dai hukumar ta kuma zafafa da kamen matasan da ke yin askin banza a Jihar, inda take tilasta musu askewa.

Kazalika, a watan Agustan da ya gabata ma Hisbah ta sanar da haramta yin amfani da mutum-mutumi domin yin tallan kayan sa wa, inda ta ce hakan kamar alamar gumaka ce.