✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jamhuriyar Nijar ta cika shekara 61 da samun ’yanci

Jamhuriyar Nijar ta cika sheakra 61 da samun ’yancin kai.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya taya takwaransa na Jamhuriyar Nijar, Mohammed Bazoum, murnar zagayowar ranar samun ’yancin kan kasar da ake yi ranar 3 ga watan Agusta.

A sanarwar daga mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar a Abuja ranar Talata, Buhari ya bayyana Jamhuriyar Nijar a matsayin “daya daga cikin manyan abokan Najeriya a Afirka”.

A cewarsa, “A koyaushe tana nuna kyakkyawar fata ga Najeriya.

“Duk da rabe-raben da ake da su a Afirka, mutanen Nijar suna da alakar al’adu da ’yan Najeriya.

“Bambancin masu mulkin mallakar mutanen Jamhuriyar Nijar bai taba hana ganin mutuncin juna da kuma ’yan uwantaka tsakaninsu da ’yan Najeriya ba.”

Buhari ya bayyana Shugaba Bazoum a matsayin “Babban dan kishin Afirka wanda ya nuna dattaku tun daga lokacin da aka zabe shi a watan Afrilu na wannan shekarar.”

Ya shaida wa Bazoum cewa: “Yayin da kuke murnar shekara 61 da samun ’yancin kan Jamhuriyar Nijar, ina muku fatan alheri a madadin gwamnati da jama’ar Najeriya.