Hukumar Kula da Samar da Guraben Karatu a Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) ta ce ya zuwa yanzu ta yi wa sama da mutum 300,000 rajistar jarrabawar UTME ta shekarar 2021.
Rahoton mako-mako da hukumar take wallafawa a shafinta na intanet ya ce zuwa ranar Litinin, sama da mutum 8,000 ne suka sayi lambobin rajistar neman gurbin shiga manyan makarantu na kai tsaye (DE).
- Ko sisi ba mu kara a kan farashin siminti ba – BUA
- Yadda mutanen gari suka kama ’yan bindiga a Zariya
Hukumar ta ce, “Adadin wadanda suka sayi lambobin rijistar UTME sun kai 344,115, masu DE kuma 10,848. Wadanda suka yi rijistar UTME kuma sun kai 316,132, yayin da masu rijistar DE suka kai 8,490.
“Yawan wadanda suka nuna sha’awar rubuta jarrabawar gwaji ta UTME kuma sun kai 126,402,” inji hukumar ta JAMB.
Hukumar ta kuma ce masu rubuta jarrabawar za su iya aikewa da lambarsu ta zama dan kasa (NIN) daga kowane layin waya matukar ba a taba amfani da shi a baya ba domin yin rajistar.
Ta ce hakan dai ya ci karo da umarnin da ta bayar da farko cewa layukan da aka hada su da lambar NIN ne kadai za a iya amfani da su wurin aikewa da NIN din tasu zuwa ga lambar 55019.
“Hanyar da ya kamata a aiki da lambar ita ce ta rubuta ‘NIN’ sannan a bayar da tazara, sannan a rubuta lambobi 14 na cikinta a aika zuwa 55019.
“Duk wata hanya da aka bi sabanin wannan wajen aikewa da lambar ba daidai ba ce.”
Jarrabawar JAMB din dai a baya ta tsara gudanarwa ranar 30 ga watan Afrilu, amma yanzu an dage ta zuwa 20 ga watan Mayu, yayin da ita kuma jarrabawar za a yi tsakanin biyar da kuma 19 ga watan Yunin 2021.
Kazalika, rijistar jarrabawar ta UTME wacce aka fara ranar takwas ga watan Afrilu yanzu za a rufe ta ranar 15 ga watan Mayu.