Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar shiga manyan makarantu a Najeriya, ta musanta rade-radin da ke yaduwa a shafukan sada zumunta da suka ambato cewa za ta sake gudanar da jarrabawar ta wannan shekara.
Cikin wani hoto da a yanzu ya karade zaurukan sada zumunta na dauke da wata sanarwa da ke cewa hukumar ce ta wallafa sakon a shafinta na Twitter na sake gudanar da jarrabawar a bana.
- Ya kamata farashin man fetur ya haura N280 —NNPC
- PDP na da yakinin samun nasara a zaben 2023 —Secondus
Sanarwar ta ce za a bai wa daliban damar sake zana jarrabawar ta bana saboda yadda wasu ke zargin an yi mummunar faduwa.
Sai dai a yayin zantawarsa da sashen Hausa na BBC, Jami’in Hulda da Al’umma na Hukumar, Fabian Benjamin, y ace yanzu haka hukumar ba ma ta amfani da shafin twitter tun bayan da gwamnatin kasar ta hana amfani da shi ballantana a ce daga wurinta sakon ya fito.
A ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni ne Hukumar ta saki sakamakon daliban da suka rubuta jarrabawar a cibiyoyin komfuta 720 daban-daban da ke fadi kasar.
Sai dai tun bayan sakin sakamakon ne mutane a zaurukan sada zumuntar zamani ke ta cewa dalibai sun mummunar faduwa musamman a yankunan Arewacin kasar.
A kan wannan jita-jita ne wasu ke ikirarin cewa kashi 10 cikin 100 ne kacal suka ci maki 200 ko fiiye a jarrabawar da aka gudanar a tsakanin ranakun 19 zuwa 22, ga watan Yuni.
A cewar Benjamin, mutanen da ke ambato alkaluman mummunar faduwar ba daga wajensu ya fito ba.
Ya ce babu wani banbanci tsakanin sakamakon jarrabawar bana da wadanda hukumar ta rika saki a shekarun baya.