Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar shiga manyan makarantu a Najeriya, ta musanta rade-radin da ke yaduwa masu ambaton cewa an samu mummunar faduwa a jarrabawar UTME ta bana.
A ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni ne Hukumar ta saki sakamakon daliban da suka rubuta jarrabawar a cibiyoyin komfuta 720 daban-daban da ke fadi kasar.
Sai dai tun bayan sakin sakamakon ne mutane a zaurukan sada zumuntar zamani ke ta cewa dalibai sun mummunar faduwa musamman a yankunan Arewacin kasar.
A kan wannan jita-jita ne wasu ke ikirarin cewa kasha 10 cikin 100 ne kacal suka ci maki 200 ko fiiye a jarrabawar da aka gudanar a tsakanin ranakun 19 zuwa 22, ga watan Yuni.
Da yake zantawa da Aminiya, Jami’in Hulda da Al’umma na Hukumar, Mista Fabian Benjamin, ya ce mutanen da ke ambato alkaluman mummunar faduwar ba daga wajensu ya fito ba.
A cewarsa, babu wani banbanci tsakanin sakamakon jarrabawar bana da wadanda hukumar ta rika saki a shekarun baya.
Kazalika, ya musanta jita-jitar da ke yaduwa kan cewa Hukumar ta shirya jarrabawar ne sabanin tsarin da ta gindaya na wasu darussa da ake zargin sun banbanta da yadda ta yi alkawarin shirya jarrabawar irinsu Adabin Turanci wato ‘Literature-in-English’.