✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

JAMB ta tsawaita wa’adin rajistar jarrabawar bana

Rajistar za ta ci gaba har zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandire a Najeriya (JAMB) ta tsawaita wa’adin rajistar jarrabawar wannan shekara da mako daya.

Hukumar ta ce ta kara wa’adin ne saboda wahalhalun da dalibai ke fuskanta wajen samun kudin rajistar, da kuma matsalolin amfanin da tsarin banki ta internet wajen sayen lambobin rajistar a yanar gizo.

JAMB din ta ce za a ci gaba da sayar da lambobin rajistar har zuwa ranar Litinin, yayin da rajistar za ta ci gaba har zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Tun da farko dai hukumar ta JAMB ta sanya ranar 14 ga watan na Fabrairun a matsayin ranar da za ta rufe yin rajistar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Dakta Fabian Benjamin ya fitar ya ce, zuwa ranar Talata hukumar ta samu mutum 1,527,068 da suka yi rajistar jarrabawar, ciki har da dalibai 168,748 da suka nuna sha’awarsu ta yin jarrabawar gwaji ta Mock-UTME.

Ya kara da cewa hukumar ta fadada karfinta, ta yadda take yi wa mutum 100,000 rajista a kowacce rana.

“Da wannan, za mu iya yi wa duka mutanen da suke da sha’awar rubuta jarrabwar ta bana rajista a cikin mako gudan da muka kara,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa “Saboda kasa da mutum 50,000 ne ke bukatar rajistar a kowacce rana, wanda ya yi kasa da adadin da hukumarmu za ta iya yi wa rajista ne a kullum ne.”