Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’o’i da Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) ta ba da sanarwar soke jarrabawar wadansu dalibai hudu da aka same su da magudin jarrabawa.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a jiya Alhamis, ta ce an soke jarrabawar ce saboda samun daliban da hannu dumu-dumu a yayin daukar jarrabawar a bara.
Shugaban Sashen Hulda da Jama’a na Hukumar, Mista Fabian Benjamin ne ya sanar da haka a wata takarda da ya sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labarai.
Ya ce hukumar ta soke jarrabawar Adah Eche wanda tun farko ya yi ikirarin an yi masa coge a sakamakon jarrabawar inda ya ce ya samu maki 290 ne amma hukumar ta yi kuskuren mayar da makin zuwa153.
Bayan dalibin ya yi wannan korafi ne ta hanyar sanar da manema labarai sai Hukumar JAMB ta gayyace shi, da aka bi diddigi sai aka gano ya tafka magudi lokacin da yake daukar jarrabawar. Da aka takura masa ne sai ya fadi gaskiyar lamari, inda ya ce lallai ya tafka magudi. Nan take hukumar ta soke jarrabawarsa tare da wadansu dalibai uku da ke da hannu a ciki.