✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

JAMB ta sauya ranar jarrabawar gwaji

Yanzu za a gudanar da jarrabawar ne a ranar Alhamis, 3 ga Yuni, 2021.

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB), ta ce daliban da suka yi rajistar jarrabawarta ta 2021 suke kuma sha’awar zana jarrabawar gwaji bisa radin kai (Mock) da su sake gurza takardar izinin jarrabawar.

Hakan na faruwa ne bayan sauyin kwanan watan zana jarrabawar da a farko aka tsara a ranar Alhamis, 20 ga wata, Mayu zuwa Alhamis, 3 ga Yuni, 2021.

Kakakin JAMB, Fabian Benjamin ya sanar cewa dole ne daliban su sake gurza takardar izinin shiga jarrabawar domin sauyin kwanan watan.

“Kamar yadda aka bayyana a baya, ana iya buga takardun izinin shiga jarrabawar daga duk inda dalibi yake da damar hakan matukar yana da damar shiga intanet,” inji shi.

Ya ce daliban za su iya gurza takardar, idan suka ziyarci wannan adireshin intanet: https://www.jamb.gov.ng annan a latsa ‘e-facility and print their slips’.

Takardar ta kunshi bayanan dalibi kamar lambar rajista, cibiyar da zai zauna jarrabawar da kuma lokacin da ake sa ran dalibin ya kasance a cibiyar.