✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

JAMB ta sauya ranar jarrabawar bana, ta tsawaita wa’adin rajistar dalibai

An tsawaita wa’adin rajistar daliban zuwa makonni biyu sakamakon kalubalen da ake fuskanta.

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantun Gaba da Sakandire (JAMB), ta ce za a fara zana jarrabawar bana daga ranar 19 ga watan Yuni zuwa 3 ga watan Yulin 2021.

Hukumar ta sauya lokacin ne sabanin na baya da ta tsara wanda ta ce za a fara jarrabawar daga ranar 5 zuwa 19 ga watan Yunin na bana.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Shugaban Hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ya fitar bayan taron masu ruwa da tsaki da suka gudanar ranar Asabar a Abuja, babban birnin kasar.

Farfesa Oloyede ya ce an kuma tsawaita wa’adin rajistar daliban zuwa makonni biyu sakamakon kalubalen da dalibai da dama suka fuskanta yayin rajistar.

A cewarsa, matakin hakan na zuwa ne domin bai wa dalibai damar kammala rajistarsu ta zana jarrabawar UTME ta bana wacce kafin yanzu ake sa ran kammalawa a ranar Asabar, 15 ga watan Mayun 2021.

“Jarrabawar UTME ta gwaji (Mock) wacce a baya aka tsara za ta gudana a ranar 20 ga watan Mayun 2021, a yanzu za a gudanar da ita a ranar 3 Yunin 2021, yayin da ita kuma ainihin jarrabawar za ta gudana a daga ranar 19 ga watan Yuni zuwa 3 ga Yulin 2021,” a cewarsa.