✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

JAMB ta dage ranar fara rajistar jarabawarta ta bana

JAMB ta dage farar rajistar jabarawarta da ta shirya kaddamarwa a 8 ga Afrilu, 2021

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta dage ranar farar rajistar jabarawarta da a baya ta shirya kaddamarwa a ranar Alhamis 8 ga Afrilu, 2021.

Mai magana da yawun JAMB, Fabian Benjamin ya ce Hukumar ta dage jarabawar ne domin kammala wasu abubuwan da suka danganci sayar da katin jarabawar.

Ya ce sanawar da Hukumar za ta fitar a kafafen yada labarai shi ne tabbacin fara rajistar, kuma sanarwar za ta kunshi bayanai dalla-dalla na yadda dalibai za su bi wajen yin rajista.

Fabian Benjamin ya bayyana cewa, “An samu jinkirin ne saboda wasu abubuwa da suka sha mana kai a kokarin da muke yi na shigar da Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN). Muna kusa shawo kan lamarin, kuma da zarar mun kammala, za a sanar da lokacin fara yin rajista”.

Kakakin na JAMB ya ba wa dalibai hakuri, yana mai cewa, “Nan ba da jimawa ba komai zai kammulu domin mu fitar da sanarwar fara rajistar dalibai”.