Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta dage ranar farar rajistar jabarawarta da a baya ta shirya kaddamarwa a ranar Alhamis 8 ga Afrilu, 2021.
Mai magana da yawun JAMB, Fabian Benjamin ya ce Hukumar ta dage jarabawar ne domin kammala wasu abubuwan da suka danganci sayar da katin jarabawar.
- An gano bom a makarantar firamare a Abiya
- Sabuwar Dokar Tsarin Neman Aure a Kano
- Dalibi ya yi dogon suma bayan yi masa bulala 6,000 a Ilorin
- Damfarar N450m: Kiristoci sun fi Musulmi tausayi —Ummi Zee-zee
- An bude tashar cajin motoci masu amfani da lantarki a Sakkwato“Da farko Hukumar ta shirya fara rajistar a ranar 8 ga Afrilu, 2021. Amma ba za mu fitar da sanarwar fara hakan ba tukuna ba sai mun tabbatar da komai ya kammala a bangaren sayar da lambar PIN da kuma amfani da manhajarmu ga daliban masu jarabawar UTME da masu DE,” inji sanarwar da ya fitar.
Ya ce sanawar da Hukumar za ta fitar a kafafen yada labarai shi ne tabbacin fara rajistar, kuma sanarwar za ta kunshi bayanai dalla-dalla na yadda dalibai za su bi wajen yin rajista.
Fabian Benjamin ya bayyana cewa, “An samu jinkirin ne saboda wasu abubuwa da suka sha mana kai a kokarin da muke yi na shigar da Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN). Muna kusa shawo kan lamarin, kuma da zarar mun kammala, za a sanar da lokacin fara yin rajista”.
Kakakin na JAMB ya ba wa dalibai hakuri, yana mai cewa, “Nan ba da jimawa ba komai zai kammulu domin mu fitar da sanarwar fara rajistar dalibai”.